Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja ta ce zaman lafiya ya fara samuwa a kananan hukumomin Rafi, Munya da Paikoro da sauransu da hare-haren ’yan bindiga suka hana su sakat.
Kwamishinan rundunar, Ogundele Ayodeji, ne ya sanar da hakan yana mai karyata labarin da ke cewa an sanya dokar hana fita a yankin Kagara da ke Karamar Hukumar Rafi.
- Uwa da ’yarta sun yi mata tsirara bayan sun casa ta
- An gurfanar da mutum 2 a gaban kuliya kan zargin wulakanta gawa
Ya kuma karyata rade-radin da ke yawo cewa ’yan bindiga sun kai wa wani shingen binciken sojoji hari a kusa da tsaunin Zuma Rock kuma suna tururuwar shiga Jihar Neja daga yankin Birnin Gwari na Jihar Kaduna.
Ayodeji ya ce an samu saukin ayyukan ’yan bindiga a Jihar Neja ne a dalilin sabbin dabarun da rundunar ta dauka na kai wa ’yan bindiga hari a maboyarsu.
Ayodeji ya ce, “Yanzu al’ummomin yankunan suna iya runtsawa da idanunsu biyu, saboda yadda muka dauki gabarar kai wa bata-garin hari, sannan ba na wasa da duk wani bayanin sirri da na samu daga jama’a saboda idan muka yi wasa da shi, har da mu zai iya runtsawa.”
Ya shaida wa ’yan jarida a hedikwatar rundunar da ke Minna cewa tun da ya kama aiki suka sauya dabarun yaki da ’yan bindiga, baya ga yawaita zagayen sintiri akai-akai da zummar dakile duk wata barazanar tsaro da masu aikata manyan laifuka.
Ya roki ’yan jaridar da sauran jama’ar jihar da su rika taimaka wa rundunar da muhimman bayanai domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Babu dokar kulle a Kagara
Kwamishinan ’yan sandan ya ce babu kamshin gaskiya a labarin da ke yawo cewa an sanya dokar hana fita a garin Kagara, hedikwatarta Karamar Hukumar Rafi ta jihar.
Ya ce “Labarin kanzon kurege ne ake yada cewa an kai wa shingen binciken sojoji hari a dutsen Zuma Rock.
“Haka ma zuki-ta-malle da ke cewa dandazon ’yan bindiga na shigowa daga yankin Birnin Gwari na Jihar Kaduna.
“Abin mamaki shi ne har masu yada labarin karyan na cewa DPO da Hukumar DSS a karamar hukumar sun tabbatar da labarin; to ku sani cewa duk wannan karya ce.
“Haka kuma babu inda aka sanya kowace irin dokar hana fita a faɗin Karamar Hukumar Rafi,” in ji shi.
Kwamishinan ’yan sandan ya yi wadannan bayanai ne bayan da farko Shugaban Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya reshen jihar, Yakubu Mustapha Bina, ya koka bisa yadda ’yan jarida ke shan wahala kafin ’yan sanda su sauraren su ko ba su bayani kan muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar jama’a.