✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfanin ruwan ‘glycerin’ a lokacin sanyi

Ruwan ‘glycerin’ na da matukar muhimmanci wajen bada kariya ga fatarmu, musanman ma yanzu lokacin sanyi. Za a iya amfani da wannan ruwa ta hanyoyi…

Ruwan ‘glycerin’ na da matukar muhimmanci wajen bada kariya ga fatarmu, musanman ma yanzu lokacin sanyi. Za a iya amfani da wannan ruwa ta hanyoyi da dama. Ruwan yana taimakawa wajen inganta fata da magance kuraje da tabo da kyasbi da sauransu. Sanyi ko hunturu kan iya zama illa ga fata, musamman fatar da ba a shafa mata mai. Ya kamata a dage wajen tsaftace jiki sosai, musamman a wannan lokacin in ba haka ba, sai mutum ya fita kamanninsa.
·         A hada ruwan ‘glycerin’ da zuma, sannan a dinga shafawa a fuska da wuya, bayan an shafa a jira zuwa tsawon minti 20 kafin a wanke da ruwan sanyi, domin magance gautsin fata a lokacin hunturu.
·         Za a iya hada wannan ruwan da madara da zuma da kuma’oats’. Hadin zai kasance kamar haka: A hada cokali daya na glycerin da cokuli biyu na zuma sannan a kwaba, daga nan a zuba madara ta ruwa, kafin a zuba ‘oats’, sai a shafa a fuska domin samun fuska da fata mai sheki.
·         Domin magance kyasbi kuwa, za a iya shafa ruwan glycerin zalla a wurin da akwai kyasbi. Za a ci gaba shafawa kullum safe da yamma har zuwa lokacin da za a rabu da kyasbi.
·         A gauraya ruwan ‘glycerin’ da kuma ruwa kadan kafin a shafa a kan tabo ko kuma ciwo. Hakan na hana fitowar tabo. Idan kuma tabo ya fito zai sanya ya bace, amma yana daukar lokaci kafin ya bace.
·         Ruwan ‘glycerin’ na magance fitowar kuraje a fuska. Za a iya shafawa a fuska a mayar da shi kamar man shafawa domin samun sakamako mai kyau.