✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amfanin cin ƙwan kifi ga lafiya

Kifi Musulmin nama!

Kifi Musulmin nama! Wasu sukan ga kifi su cinye namansa tsaf amma idan suka ga kwan kifin sai su ture.

Kwan kifi yana da matukar alfanu ga lafiyarmu. A kasashen Yammacin Duniya kwan kifi ya ma fi naman kifi tsada saboda ribibinsa ake ganin amfanin da ke cikinsa.

Kwayayen kifi su ne wadannan dunkullallun nama kanana da akan samu a macen kifi wadanda za a iya gani a cure ko dai bakake ko ruwan toka ko ma jajaye a wani launin kifayen.

Idan aka dafa ko aka soya suna da wani irin gardi a baki da kaushi, ba laushi ba. Suna nan idan an tauna su za a ji su gurus-gurus.

Bincike ya nuna duk wani sinadari da ake samu a cikin kifi to ana samu a cikin kwayayen kifi har ma da kari.

Ban da sinadarin protein na kifi da man kifi na omega 3 mai kara lafiya ga zuciya da bitaman na rukunin D da da sinadarin calcium da ke cikin tsokar kifi, a cikin kwayayen akwai wadannan da ma sinadarai na bitamin ajin A da B mai tsadar ma wato B12 da sinadarin ma’adinai irin su selenium da phosphorus da sinadarin folate da choline mai inganta lafiyar hanta da ta laka, sai sinadaran lutein da zeadanthine masu kara lafiyar gani da sauransu.

A abinci kalilan ne ake samun irin wadannan sinadarai masu kara lafiya a cure a wuri guda haka.

Mun san cewa a yanzu masu sana’ar sayar da kifi sun ninka kudin kifi haka kawai har ya fi na dabbobin tudu, to kada su ji wannan batu kuma su ce za su ninka mana kudin kwayayen kifi.