✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfani da jiragen kasa zai sa tasoshin Teku-Huta aiki cikin nasara – Usman

Manajan Daraktar Hukumar Kula da Tasoshin Ruwa ta Najeriya (NPA), Hajiya Hadiza Bala Usman ta ce yin amfani da jiragen kasa wajen sufuri zai tabbatar…

Manajan Daraktar Hukumar Kula da Tasoshin Ruwa ta Najeriya (NPA), Hajiya Hadiza Bala Usman ta ce yin amfani da jiragen kasa wajen sufuri zai tabbatar da nasarar ayyukan tashoshin Teku-Huta yadda ya kamata. Hadiza Bala Usman, ta bayyana haka ne a taron masu ruwa-da-tsaki don wayar da kan jama’a game da ayyukan Tashar Teku-Huta ta Kaduna, wadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar kwanakin baya.

Shugabar ta NPA, wacce Kyaftin Ihenacho Ebubeogu ya wakilta a taron, ta ce kasar nan ba za ta samu nasarar dorewar aiki da tasoshin Teku-Huta ba, sai in tana amfani da jiragen kasa wajen safarar kayayyaki.

Ta ce, “Dole ne harkokin sufurin kasar nan su ta’allaka a kan jiragen kasa. Bayan samun mulkin kai, Najeriya ta yi watsi da harkar sufurin jiragen kasa, duk da cewa shi ne ginshikin inganta sufuri baki daya, yayin sauran harkokin ke rufa masa baya.”

Haka kuma ta nanata cewa harkokin dakon kaya abu ne maras iyaka, inganci da kuma gasar farashi sannan masu gudanar da tashar ta Kaduna su tabbatar cewa za su bai wa wadannan abubuwa muhimmanci. Ta kuma ce, dole ne a dasa tasoshin a inda suka dace, a yayin kuma da take jinjina wa Tashar Teku-Huta ta Kaduna bisa shirya wannan taro wanda alfanunsa zai dauki tsawon lokaci a sha’anin tasoshin kasar nan.