Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Filato (SEMA), Alhaji Alhassan Barde ya ce ambaliyar ruwa ta hallaka mutum 10 tare da lalata gidaje 1,153 daga watan Mayu zuwa watan Yunin bana a jihar.
Alhaji Alhassan Barde ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a garin Jos fadar jihar, inda ya ce kananan hukumomin jihar da ambaliyar ruwa ta shafa sun hada da Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Bokkos da Kanke da Wase da Shendam da Mikang da Jos ta Gabas da Langtang ta Arewa da kuma Langtang ta Kudu. Sakataren ya ce, hukumarsa tana yin iyakar kokarinta wajen ganin ta tallafa wa wadanda ambaliyar ta shafa.
“A watan Mayun da ya gabata mun gano cewa ambaliya ta hallaka mutum 10 tare da lalata gidaje 1,153. Wannan ambaliya ta shafi kauyuka 832 a kananan hukumomin jihar 17,” inji shi.
Ya ce nan ba da dadewa ba za su shiga dukan kananan hukumomin da ambaliyar ta shafa, domin gane wa idanunsu halin da wadanda lamarin ya shafa suke ciki. Kuma su ji abubuwan da suke bukata domin su zo su samu gwamnatin jihar a san yadda za a yi a tallafa musu.