✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cutar Kwalara ta kashe mutum 50 a Yobe

Cutar ta kuma kama sama da mutum 1,000 a jihar

Akalla mutum 50 ne annobar cutar Kwalarar da ta barke a jihar Yobe ta halaka, cikin mutane sama ca 1,000 da suka kamu da ita a jihar.

Hakan ya faru ne sanadiyyar ambaliyar ruwan sama da aka samu a daminar bana, wacce ta raba mutane da yawa da muhallinsu, ta kuma gurbata ruwan sha.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Mohammed Lawan Gana ne tabbatar da hakan yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Damaturu, babban birnin jihar.

Dokta Gana ya ce an samu labarin bullar cutar tare da yaduwarta a sassan da ambaliyar ruwa ya fi shafa, ciki har da Damaturu babban birnin jihar.

Sannan ya ce duk da yawan mace-macen da aka samu, cutar ba ta yi irin illar da ta yi ba a shekarar da ta gabata.

Kwamishinan ya alakanta hakan da daukar matakan gaggawa da ya ce gwamnatin jihar ta yi, da kuma taimakon kungiyoyin bayar da agaji na ciki da wajen jihar.

Kazalika, ya ce ma’aikatarsa na cikin shiri tun ma kafin rahoton bullar cutar.

Ya kuma ce matakan da aka dauka sun taimaka matuka wajen rage barnar da aka yi fargabar samu a yankunan da abin ya shafa a fadin jihar.