✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliyar ruwa ta yi barna a sansanin sojoji da ke Borno

Ambaliyar ta mamaye ilahirin sansanin sojojin

Wata ambaliyar ruwa ta jefa dakarun sojan Najeriya cikin halin kaka-ni-ka-yi a sansaninsu da ke Malam Fatori a Jihar Borno.

Yankin da sansanin yake dai yana kusa da kogin Komadougou Yobe da kuma gabar Tafkin Chadi, ta Abadam kuma yana kan iyaka da kasashen Chadi da Jamhuriyar Nijar.

Matsalar ambaliyar dai ta kara dagula yanayin hamada da sojojin ke ciki wajen fafatawa da ’yan ta’addan ISWAP da ke da sansanoni a yankin da ke kusa da Tafkin Chadi.

Sojojin da ke garin sun yi suna da jarumta wajen tinkarar hare-haren da ake kai musu daga mayakan ISWAP da ke aiki da makamai iri-iri da suka hada da bama-bamai da gurneti da kuma manyan motocin da ke dauke da bindigogin yaki.

Masanin tsaron nan da ke yankin Tafkin Chadi, Zagazola ya fahimci cewa makonni da dama da ambaliyar ruwan, daruruwan mazauna yankin musamman ma ’yan gudun hijira, na kokawa kan samun matsuguni, abinci da sutura tare da neman mazaunin da ke karkashin yanayin tsoro.

Galibin sassan garin na malam Fatori yanzu haka dai ba ya shiguwa saboda ambaliya ruwan da ta mamaye akasarin yankin.

%d bloggers like this: