✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Jigawa

Mun tanadi sansanonin 'yan gudun hijira.

Akalla mutum 50 ne suka rasa rayukansu da yawa kuma sun kaurace wa gidajensu sanadiyyar ambaliyar ruwa a Jihar Jigawa.

Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa na jhar ne ya bayyana wa manema labarai hakan ranar Lahadi a Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa, ambaliyar ta tagayyara dubban gidaje wanda hakan ya tilasta mazauna yankin yin gudun hijira zuwa wasu gine-ginen gwamnati.

Shugaban ya ce, gwamnati ta bude sansanoni 11 na ‘yan gudun hijira, a yayin da kuma ake gargadin mazauna wuraren da ke kusa da koguna da sauran magudanar ruwa da su sauya mastsugunai a sakamakon fargabar karin ambaliyar sanadiyyar ruwan sama na mamako da ke sauka a daminar bana.

Wadanda ambaliyar ta shafa sun hada da mazauna kauyukan Balangu wanda kimanin gidaje 237 ne ambaliyar ta lakume yayin da hudu suka rasu.

” Muna da ‘yan gudun hijira da yawa a sansanonin wucin gadi 11 a Balangu kadai, gidaje 237 sun lalace sannan mazauna gidajen sun koma sansanin  da aka ware masu,” in ji shi.