Akalla mutum 50 ne suka rasa rayukansu da yawa kuma sun kaurace wa gidajensu sanadiyyar ambaliyar ruwa a Jihar Jigawa.
Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa na jhar ne ya bayyana wa manema labarai hakan ranar Lahadi a Dutse, babban birnin jihar.
- Za mu maido da shingen bincike —’Yan sanda
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sojoji Suka Shiga Wurin ’Yan Ta’adda Suka Ragargaje Su —Ganau
Ya bayyana cewa, ambaliyar ta tagayyara dubban gidaje wanda hakan ya tilasta mazauna yankin yin gudun hijira zuwa wasu gine-ginen gwamnati.
Shugaban ya ce, gwamnati ta bude sansanoni 11 na ‘yan gudun hijira, a yayin da kuma ake gargadin mazauna wuraren da ke kusa da koguna da sauran magudanar ruwa da su sauya mastsugunai a sakamakon fargabar karin ambaliyar sanadiyyar ruwan sama na mamako da ke sauka a daminar bana.
Wadanda ambaliyar ta shafa sun hada da mazauna kauyukan Balangu wanda kimanin gidaje 237 ne ambaliyar ta lakume yayin da hudu suka rasu.
” Muna da ‘yan gudun hijira da yawa a sansanonin wucin gadi 11 a Balangu kadai, gidaje 237 sun lalace sannan mazauna gidajen sun koma sansanin da aka ware masu,” in ji shi.