Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Yobe sun tabbatar da mutuwar mutane biyar yayin da gawarwaki biyu suka bace sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a Karamar Hukumar Potiskum ta jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, ambaliyar ruwan ta auku a sassa da dama na garin Potiskum biyo bayan mamakon ruwan sama da aka tafka a daren Lahadi.
- Mamayar Taliban: Shugaban Afganistan ya ranta a na kare
- ‘Yan Boko Haram 190 sun sake mika wuya a Borno
Wani mazaunin yankin mai suna Hamza Maidede, ya ce gine-gine da yawa a kewayen al’ummomin Nahuta sun rushe tare kari a kan kadarori da dama da suka salwanata.
Maidede ya ce “A halin yanzu muna cikin bakin ciki saboda wani jariri a unguwar ya rasa ransa yayin da gini ya rufta a kansa.
“Muna addu’ar Allah ya kare mu baki daya sannan muna neman dauki daga gwamnati a dukkan matakai”.
Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Dokta Mohammed Goje ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce a halin yanzu tawagar bincike da aikin ceto na SEMA suna Potiskum inda suke gudanar da bincike tare da taimaka wa al’umma a kokarin gano gawarwakin da suka bace.
Goje ya kara da cewa, ana ci gaba da aiwatar da wani shiri na sauya matsugunin mazauna yankuna da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a Damaturu kamar yadda gwamnan jihar ya umarta.
Aminiya ta yi kokarin neman karin bayani daga bakin babban jami’i na Karamar Hukumar Potiskum, Salisu Muktari ta wayar tarho, inda ya ce a tuntubi hukumomin da suka dace don samun cikakken bayani.