Fiye da mutum 50 sun riga mu gidan gaskiya a sakamakon ambaliyar ruwan da ta yi mummunar barna a Jihar Jigawa.
Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa na jihar (SEMA), Sani Yusuf ya ce ambaliyar ruwan ta daidaita mutane da dama.
- LABARAN AMINIYA: Ba Lallai Mu Kara Zaman Tattaunawa Da Gwamnatin Buhari Ba – ASUU
- Bene mai hawa uku ya danne mutane da dama a kasuwar wayoyi ta Kano
A cewarsa, mutum sama da 2,051 ambaliyar ta daidaita a kauyen Karnaya da ke Dutse, babban birnin jihar.
Ya ce gwamnatin jihar na shirin kai uwaye 404 da ’ya’yansu da suka kai 1,334 zuwa sansanin ’yan gudun hijira na Warwade.
Haka kuma ya ce maza 313 za su ci gaba da zama a wata makarantar firamare da ke kauyen kafin ambaliyar ta ragu.
Sani Yusuf ya kara da cewa, suna kuma bukatar agaji saboda ambaliyar na ci gaba da shiga kauyuka, inda gadoji da dama suka karye, lamarin da ya gargadi direbobi da su kiyaye yayin tuki.
Ya kuma ce gwamnatin jihar ta mika wa Gwamnatin Tarayya wani rahoto, inda take bukatar taimako wajen takaita ambaliyar ruwan.
Aminiya ta ruwaito cewa, an yi asarar dukiya ta miliyoyin nairori sakamakon ambaliyar ruwa da ta afka wa kasuwar Kantin Kwari da ke Jihar Kano a ranar Litinin.
Ruwan saman da aka yi shi kamar da bakin kwaira na ranar Litinin ne ya dada tayarwa da ‘yan kasuwar hankali yayin da ya yi ambaliyar ta cika kwatoci da magudanan ruwa, ta kuma kwarara har cikin shagunan jama’a.
Da yawa daga cikin ‘yan kasuwar na dora alhakin ambaliyar akan gwamnati a bisa gine-ginen da ta yi cikin kasuwar da kuma manyan layukan da sayar da su, wanda suka toshe magudanan ruwa.
Bugu da kari, ginin gadar sama da gwamnatin ke yi, ta yi shi ne kan babbar magudanunar ruwa, da ruwansu ke fitowa daga unguwannin Gyadi-gyadi da Sabon titi da Mandawari ya ratsa ta Fagge.
Sai dai gwamnatin tana dora alhakin ambaliyar kacokam kan dan kwangilar da ke aikin hanyar gadar saman.