Gwamnatin jihar Neja ta ce akalla yankuna 17,000 ne ambaliyar ruwa ta yi wa mummunan ta’adi a jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Ahmad Matane shine ya tabbatar da hakan ta bakin jami’in watsa labaransa, Tanko Lawal a cikin wata sanarwa ranar Litinin.
Ya ce sakataren ya bayyana hakan yayin wata ziyarar gani da ido domin kiyasta barnar da ambaliyar ta yi a karamar hukumar Mokwa ta jihar.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa yankunan da lamarin ya shafa a kananan hukumonin Mokwa, Lapai, Edati, Lavun, Shiroro, Munya da Wushishi suke.
Ya kuma ce sama da mutane 60,000 ne ambaliyar ta shafa wanda ya kai ga rushewar gidaje da shafe gonaki da dama a karamar hukumar ta Mokwa.
Sakataren gwamnatin ya kuma ce tuni gwamnatin jihar ta fara raba buhuna 2,400 na hatsi a matsayin kayan tallafin abinci domin rage radadi ga wadanda iftila’in ya shafa.
A nasa jawabin, Kuta na masarautar Kede Alhaji Muhammad Muregi da kuma hakimin Jaagi, Alhaji Yahaya Aliyu, kira suka yi ga gwamnati kan ta kai musu dauki saboda yawancinsu sun rasa muhallansu.