Wata ambaliyar ruwan da ta biyo bayan mamakon ruwan sama ta yi sanadiyyar rushewar gidaje akalla 350 a wasu yankunan karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato.
Kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar, Abubakar Ghani, wanda ya tabbatar da alkaluman ya kuma ce matsalar ta raba mutane da dama da muhallansu.
- LABARAN AMINIYA: Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalin Mutum 50 A Jigawa
- William Ruto ya lashe zaben Shugaban Kasar Kenya
Ya ce ambaliyar ruwan ta auku ne a karshen mako, inda ta shafi kauyukan Shiyar Ajiya da Makera da kuma Runji.
Abubakar ya kuma ce Shugaban hukumar, Alhaji Zubairu Magaji, ya kuma ce akalla gidaje 250 ne suka rushe a yankunan sakamakon ruwan saman.
Sai dai ya ce ba a sami asarar rai ba ko daya, amma ambaliyar ta yi awon gaba da kayan abincin mutane masu yawa.
Shugaban hukumar ya kuma ba mutanen da lamarin ya shafa cewa gwamnati za ta tallafa musu nan ba da jimawa ba.
Shi ma Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar ta Tangaza, Ibrahim Lawal, ya yaba wa Gwamnatin jihar saboda waiwayar jama’ar tasu a yanayin da suke ciki, tare da rokon a tallafa wa wadanda lamarin ya raba da muhallansu kuma ba su da abinci.