Hukumar Sibil Difens a Jihar Jigawa, ta sanar da cewa ambaliyar ruwa ta raba aƙalla mutum 100 da gidajensu a garin Gantsa da ke Ƙaramar Hukumar Buji.
Mai magana da yawun hukumar, ASC Badaruddeen Tijjani, ya bayyana cewa hakan ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a ranar Lahadi.
- Tinubu ya sa hannu kan dokar ninka wa alkalai albashi sau uku
- An kashe likita, an sace mutane 8 a Kaduna
Ya ce ruwan ya lalata gidaje sama da 100 a garin, inda ya tilasta wa mutanen da abin ya shafa barin gidajensu.
Ambaliyar ta jawo asarar dukiyoyi masu tarin yawa, inda mutane da dama suka rasa wajen zama.
Hanyoyin ruwa na garin sun yi cika maƙil da ruwa, lamarin da ya jawo ambaliyar ruwa ta mamaye ko ina garin.
Jami’an ƙaramar hukumar, hukumomin tsaro, da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar, sun fara taimakon mutanen da abin ya shafa.
Ya zuwa yanzu dai an fara kai wa jama’ar da lamarin ya shafa agaji, da kuma tallafi.
Haka kuma, an tura jami’an NSCDC zuwa yankin don ba su tsaro da kuma ba su agajin da suke buƙata.
Kwamandan NSCDC na jihar, Muhammad Danjuma, ya ƙuduri aniyar tabbatar da tsaron mutanen da ambaliyar ta shafa.
Sai dai ya shawarci mazauna garin su ƙara sanya ido tare da kula a lokacin damina don rage afkuwar ambaliyar ruwa.
Kazalika, ya buƙace su da su riƙa bibiyar bayanan yanayi da bin umarnin hukumomi don gujewa afkuwar wani mummunan lamari nan gaba.