Ambaliyar ruwa ta lalata yankuna 225 a Kananan Hukumomi 31 da ke Kano da Jigawa a cewar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA).
Babban jami’in NEMA mai kula da Kano da Jigawa, Dokta Nuradeen Abdullahi ne ya sanar hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Asabar.
- Dalilin da sojoji fiye da 200 za su ajiye aiki —Nwachukwu
- Yadda gobarar daji da fari ke neman durkusar da kasashen Turai
A cewarsa, ambaliyar na da nasaba ne da ruwan sama na mamako da ake tafkawa tun daga watan Yuli zuwa yanzu.
Ya ce wannan yanayi wanda ba yanzu aka soma fuskantarsa ba, ya tilasta wa mutane da dama rasa matsugunai da hijira zuwa wasu yankunan a Arewacin kasar.
Kananan hukumomin da ambaliyar ta shafa a Kano sun hada da Tudun Wada, Doguwa, Kibiya, Kiru, Gwale, Danbatta, Bagwai, Ajingi, Albasu, Shanono, Tsanyawa, Rimin Gado da Dawakin Kudu.
A Jigawa kuma akwai kananan hukumomi irinsu, Kafin Hausa, Malam Madori, Hadejia, Guri, Auyo, Birniwa, Jahun, Miga, Kiyawa, Birnin Kudu, Kaugama, Babura, Gwaram, Dutse da Kirikasamma.
Abdullahi ya ce ambaliya ta lalata gidaje da gine-gine da gonaki da wajen kiwo da sauran tarin dukiyoyi.
A kwanakin baya ne aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya lalata yankuna da dama a jihohin Kano da Jigawa, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi na miliyoyin naira.
Aminiya ta ruwaito cewa, ambaliyar ruwan na zuwa ne a yayin da NEMA ke ci gaba da gargadin masu ruwa da tsaki da su dauki matakan da suka dace domin kaucewa ambaliyar ruwa da ke addabar al’umma daban-daban a halin yanzu.
A farkon wannan watan ne Hukumar Hasashen Yanayi (NiMet) ta sanar da cewa, ana sa ran saukar ruwan sama kusan duk rana a jihohin Arewa 19 ciki har da Kano da Jigawa a tsakanin Agusta zuwa Satumban 2022.