✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 14,940 a Sakkwato 

Kwamitin ya buƙaci gwamnatin jihar ta ɗauki matakin da ya dace cikin gaggawa.

Aƙalla gidaje 14,940 ne suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Sakkwato.

Shugaban kwamitin taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa a jihar, Muhammad Bello Idris ne, ya bayyana haka yayin miƙa rahoton kwamitin ga Gwamna Ahmed Aliyu a ranar Litinin.

Ya ce ƙauyuka 1,341 a ƙananan hukumomi 22 ne, ambaliyar ruwan ta shafa a bana.

Ambaliyar ta lalata gonaki 11,390 da kuma amfanin gona mai yawa.

Bugu da ƙari, ambaliyar ta lalata dam 50, tafkunan ruwa 250, hanyoyin magudanun ruwa masu tsawon kilomita 60, da lalata wasu wurare sama da 1000.

Kwamitin ya bayar da shawarar a bai wa waɗanda abin ya shafa taimakon gaggawa, tare da samar da jiragen ruwa domin jigilar waɗanda lamarin ya shafa.

Kazalika, kwamitin bayar da shawarar cewa gwamnatin jihar tare da tallafin ƙasa da na ƙasashen duniya su mai da hankali kan gina hanyoyin ruwa, tsaftace su da kuma gyara muhimman wuraren da ambaliyar ruwa ke kawo cikas ga dam-dam.

Gwamna Aliyu, ya gode wa kwamitin game da aikinsu, tare da alƙawarin cewa zai duba shawararsu da kuma aiwatar da su.