Hukumomin Kasar Afirka ta Kudu sun ce, adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a birnin Durban ranar Talata ya zarce 250, yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka bata.
Babbar jami’ar kula da lafiya a yankin da aka samu iftila’in Nomangugu Simelane-Zulu ta tabbatar da wannan sabon adadin, inda take cewa ya zuwa daren jiya sun aje gawarwakin mutane 253 a asibitocin su guda biyu.
- Matawalle ya yi martani kan raba wa Sarakunan Zamfara motoci na alfarma
- A kori Minista da mashawarcin Buhari kan tsaro —’Yan Majalisa
Jami’ar ta ce ya zuwa wannan lokaci suna cikin fargaba, domin dakin ajiye gawarwakin ya cika ya batse, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto.
Shugaban kasa Cyril Ramaphosa wanda ya ziyarci yankunan da aka samu hadarin ya ce da sun saba ganin iftila’in na afkawa wasu kasashe irinsu Mozambique da Zimbabwe, amma yau gashi suna gani a gida.
Rahotanni sun ce an kwashe shekaru 60 ba a taba ganin irin ruwan saman da aka gani ranar Talatar ba, wanda ya rusa gidaje da gadoji da wanke hanyoyi da kada turaku da kuma tarwatsa kwantainoni a tashar jiragen ruwan kasar.