✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliyar ruwa ta kashe fiye da mutum 1,000 a Pakistan

Shugaba Buhari ya ce ’yan Najeriya na ci gaba da taya ’yan Pakistan da addu’a.

Yawan mutanen da ambaliyar ruwa ta hallaka a kasar Pakistan sun haura dubu daya kamar yadda alkaluman da mahukuntan kasar suka fitar a Lahadin nan.

Gwamnatin Pakistan ta nemi taimakon kasashen duniya a sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar rayukan mutum fiye da dubu daya.

Tuni gwamnatin kasar ta ayyana dokar ta baci a yayin da Firaiminista Shahbaz Sharif ya yi kira ga manyan kasashen duniya da su kawo wa kasar dauki.

Mutum sama da miliyan talatin daga cikin al’ummar kasar na cikin yanayi na bukatar taimako a sakamakon bala’in ambaliyar ruwa.

Akasarin ’yan kasar sun ce ba su taba ganin irin ambaliyar ruwan ba duk da cewa ba sabon abu ba ne a kasar.

Sai dai bayanai sun ce ruwanbana ya sauka ninkin yadda aka saba gani a cikin watan Augustan kowacce shekara a Pakistan.

Pakistan tana bukatar dauki —Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da ambaliyar ruwan ‘mafi tsanani’ a tarihin Pakistan, yana mai nema wa kasar tallafi daga hukumomin duniya.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa daga Fadar Shugaban Kasar ta ta fitar tana mai cewa ambaliyar ta kashe mutum fiye da 1,000 tare da lalata gidaje da tituna da gadoji.

“Shugaba Buhari ya ce ’yan Najeriya na ci gaba da taya ’yan Pakistan da addu’a yayin da suke fuskantar wannan bala’i mai girman gaske,” a cewar Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaban Kasa.

Buhari ya roki Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji su taimaka wa “jama’ar da ruwa ya raba da muhallansu” da kuma “tallafa musu da abinci yayin da miliyoyi ke bukatar agaji.”