✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliya: IFAD ta ba da tallafin $5m don taimaka wa manoman Najeriya

IFAD ta ba da tallafin don rage wa manoma radadin iftila'in ambaliyar ruwa.

Asusun Bunkasa Noma na Kasa da Kasa (IFAD) ya sanar da bayar da wani sabon tallafin Dalar Amurka miliyan biyar ga gwamnatin Najeriya domin taimaka wa manoman da ambaliyar ruwa ta lalata wa gonaki.

Mataimakiyar Shugaban IFAD, Misis Katherine Meighan ce, ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin wata ganawa da Ministan Noma da Raya Karkara, Dokta Mohammad Mohmood Abubakar a Abuja.

Taron wanda aka gudanar a Ma’aikatar Harkokin Waje wani bangare ne na ziyarar aiki ta kwanaki biyu da Misis Meighan ta kawo Najeriya.

“Zan fara da nuna alhinina da kuma goyon ga al’ummar Najeriya dangane da ambaliyar ruwa da ta yi barna a baya-bayan nan, wadda ta haddasa munanan asarar rayuka da amfanin gona da kuma dabbobi.

“Kuma ina yaba muku da gwamnati kan zuba jarin da kuka yi a harkar noma, domin na amince da ku kan muhimmancin samar da abinci da kuma ci gaba da bunkasa noman cikin gida.

“Na yi matukar farin cikin sanar da karin tallafin Dala miliyan biyar don shirin bunkasa tare da habaka harkar noma,” in ji ta.

Misis Meigha ta ce IFAD ta yi aiki tare da gwamnatin Najeriya don mayar da hankali sosai musamman kan kananan manoma da ke yankunan karkara wadanda suke  noman kayan abinci,” ta kara da cewa “yayin da ruwa ke ja da baya, muna kuma taimakawa wajen kula da gonaki da kuma yin shuka.”

Da yake mayar da martani, Dokta Mohmood ya gode wa jami’ar ta IFAD a madadin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa sabon tallafin kudi da kuma alkawarin taimaka wa manoman Najeriya kan yadda ambaliyar ruwa ta ja musu asarar dukiya mai tarin yawa.”