✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa da rikicin Boko Haram ne suka haddasa hauhawar farashin wake – Shu’aibu Madobi

A dan tsakanin nan wake shi ne nau’in kayan abinci mafi tsada wanda ake amfani da shi  a kasuwannin qasar nan.  Aminiya ta bi diddigin…

A dan tsakanin nan wake shi ne nau’in kayan abinci mafi tsada wanda ake amfani da shi  a kasuwannin qasar nan.  Aminiya ta bi diddigin musababbin hauhawar faranshin waken inda ta yi hira da Malam Shu’aibu Isiyaku Madobi wanda ke hada-hadar wake a Kasuwar Ilepo a Legas, ya kuma bayyana cewa ambaliyar ruwa a yankunan Jihar Neja a bara da rikicin boko Haram a Jihar Barno ne musababbin tsadar wake a bana.

Ya ce Jihohin Barno da Neja ne suka  fi samar da wake a qasar nan “Matsalar ambaliyar ruwa a Jihar Neja a bara da rikicin Boko Haram sun janyo qarancin wake a kasuwannin qasar nan lamarin da ya sa ya yi tsadar da ba a taba ganin irin ta a baya ba. Duk da yake waken nau’in daban-daban ne amma dukkan su farashin su ya haura. Irin nau’in daban-daban ya fi daraja a yanzu ana kiran sa durom shi yakan zo mana a buhu abin da ya kama daga Naira dubu 44 har zuwa dubu 46,  shi kuma Oloyin ya kan zo mana a kan Naira dubu 40 zuwa dubu 42 ya danganta da yadda kasuwa ta kama.   Sai farin wake da buhun sa yake zuwa mana a kan Naira dubu 32.” 

Shu’aibu Madobi ya qara da cewa baya ga ’yan Najeriya har maqwabta qasashen qetare kan shigo sayan waken su tafi da shi qasashen su,  sai dai a yanzu masu sayan wake sun ragu qwarai duba da tsadar da ya yi domin a yanzu ya fi shinkafa tsada. Wani abu da yake kawo mana cikas kuma shi ne yadda jami’an gwamnatin Legas ke kame mana yaran da suke tallar waken a kan baro.  

“A baya akwai wadanda kan sayi kamar buhu 20 ko 40 a kowacce rana a wajan mu,  sai su rarrabawa yaran su wadanda kan kewayawa da shi a baro sai dai tun bayan da gwamnatin Legas ta kafa dokar hana tura baro a Legas idan yaran suka fita ana kame su inda ake sanya masu tara mai yawa,  amma babu abin da za mu yi sai dai mu yi wa Allah godiya,  amma ka ga idan ana sayan abu sossai ko da ribar sa babu yawa mutuqar ana saya a-kai-a-kai sai ka ga Allah Ya sanya masu albarka.”

A qarshe Malam Shuaibu Madobi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bai wa manoma kulawar da yakamata ganin yadda damina ke qaratowa domin a kai ga samun yabanya mai albarka.