Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta bayar da tallafin naira miliyan 10 domin rage radadin mutanen da suka fuskanci ambaliyar ruwa a Jihar Binuwai.
Aminiya ta ruwaito cewa, Aisha Buhari ta ba da tallafin ne ta hannun mai dakin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Sanata Oluremi Tinubu.
- Kotu Ta Ba Da Umarnin Tsare Shugaban EFCC A Gidan Yari
- Iyayen yaran da maganin tari ya kashi sun yi watsi da diyyar Dala 1.4m
Bayanai sun ce Aisha Buhari ta ce a raba tallafin a tsakanin mutane 200 da ambaliyar ruwa ta janyowa asarar muhallai da dukiya a Makurdi, babban birnin jihar.
Tuni dai Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (SEMA) a Binuwai, ta ce an raba tallafin ga wadanda ibtila’in ambaliyar ya rutsa da su.
Babban Sakataren SEMA, Dokta Emmanuel Shior ya ce sun raba kudin ne ga kauyuka biyar da abin ya fi shafa a Makurdin.