✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar Lokoja ce ta haddasa karancin man fetur a Abuja —IPMAN 

Mahukunta sun danganta matsalar karancin man fetur din da ambaliyar ruwa ta afku a Lokoja.

Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN), Debo Ahmed, ya ce har yanzu man fetur na kara karanci a Babban Birnin Tarayya Abuja da kewaye, bayan da ambaliyar ruwa da ta haddasa cinkoson ababen hawa a Lokoja, Jihar Kogi, wanda hakan ya haddasa tsaikon zuwan man. 

Tun farkon watan Oktoba, aka fara samun dogayen layuka a gidan mai a Abuja, inda gidajen mai da dama suka rufe.

Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta ce ambaliyar ta mamaye manyan tituna a Lokoja tare da haddasa karancin man fetur.

Amma ’yan kwanaki bayan nan ambaliyar ruwan ta ragu, karancin man fetur din na ci gaba da ta’azzara a Abuja da kewayenta.

Shugaban kungiyar ta IPMAN ya danganta matsalar karancin man din da ake fuskanta a halin yanzu da tsaikon jigilar man zuwa inda ake bukata.

“Su (masu kawo kayan) sai sun sauke a gidajen mai wanda kafin su sauke mutane sun taru, wanda hakan yake sa wasu su dauka ko ana fuskantar karancin mai ne wanda ba haka abun yake ba.

“Akwai man fetur mai tarin yawa a dafo-dafo, kawai ana samun matsala ne a kan hanyar da ake jigilarsa.”