✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar Kebbi na barazana ga samar da abinci —Buhari

Shugaban Muhamamdu Buhari ya ce yawan ambaliya ruwan sama a Jihar Kebbi na yin babbar barazana ga yunkurin samar da wadataccen abinci a Najeriya. Buhari…

Shugaban Muhamamdu Buhari ya ce yawan ambaliya ruwan sama a Jihar Kebbi na yin babbar barazana ga yunkurin samar da wadataccen abinci a Najeriya.

Buhari ya jajanta kan ambaliyar da ta yi ajalin rayuka da dukiyoyi baya ga share dubban hektoci na amfanin gona, yana mai cewa lamarin ya jefa Najeriya a cikin barazana.

“Na damu matuka musamman game da wannan al’amari saboda ya kawo tangarda ga kokarin bunkasa noman shinkafa domin hana shigowa da abinci daga ketare”.

Da yake ta’aziyya ga iyala mamatan, Buhari ya ce Gwamantin Tarayya za ta yi aiki tare da gwamnatin Jihar Kebbi wajen tallafa wa wadanda suka yi asara a ambaliyar.

“Mun mayar da hankali sosai a kan Jihar Kebbi a shirinmu na samar da wadatacciyar shinkafa ‘yar gida da nufin farfado da darajar noma da a baya aka yi watsi da ita.

“Asarar rayukan mutum shida da da dubbban hektoci gonakin shinkafa na sama da Naira biliyan daya a Jihar Kebbi, ta kawo babbar cikas ga shirinmun na samar da abinci wadatacce.

“Wannan abu ya yi muni sosai kasancewar manomansu da sauran ‘yan Najeriya na fatan samun amfani mai yawa a bana domin rage tsadar kayan abinci a kasuwanni”, inji sananrwar da mai magana da yawunsa, Garba Shehu.