Ma’aikatan ceto na ci gaba da neman sama da mutum 70 bayan ambaliyar ruwan sama da zaftarewar kasa sun hallaka sama da mutum 150 a kauyakan kasashen Indonesiya da East Timor.
Mahaukaciyar guguwar Seroja da ta haddasa ambaliyar da zaftarewar kasar ta kuma raba fiye da mutum 10,000 da muhallansu a kasashen masu makwabtaka da juna.
- Sojoji na samun nasara a yaki da Boko Haram —Zulum
- Damfara ta miliyan N450 aka yi rana guda —Ummi Zee-Zee
- Rana ba ta karya: Ranar sake bude sufurin kasa da kasa a filin jirgin saman Kano ta zo
Ambaliyar gami da laka da mahaukaciyar guguwar sun tuge bishiyoyi tare da shafe kauyuka a Indonesiya da East Timor, inda asibitoci da gadoji da gidaje suka rushe.
Lamarin da ya tilasta wa mazauna yin kaura zuwa kasashe makwabta a yankin Kudu maso Gabashin Asiya.
Hukumar Kula da aukuwar Iftila’ai ta Indonesiya ta tabbatar da rasuwar mutum 130 a wasu kauyuka da ke kusa da iyakarta da kasar East Timor, inda hukumomi suka sanar da mutuwar mutuwar wasu mutum 27.
Ma’aikatan ceto na kokarin nemo wasu mutum 70, inda suke ta fadi-tashin tona baraguzan gine-gine da suka rushe a tsibirin Lembata da ke gabar teku.
Hukumomi sun ce suna kokarin samar wa mutanen da aka ceto daga yankunan da kuma tabbatar da hana yaduwar cutar COVID-19.
“Mutanen sun tsira ne daga su sai ’yan tufafinsu da suka iya goyawa a bayansu; Suna bukatar a samar musu da tantuna da barguna da katifu da matassai” inji Mataimakin Magajin Garin yankin, Thomas Ola Longaday.
A halin yanzu dai, yankin na Lembata na fuskantar kalubale a cibiyoyin kula da lafiyansa, da za su kula da mutanen da suka samu raunuka da ke ta karuwa.
“We don’t have enough anaesthesiologists and surgeons, but we’ve been promised that help will come,” Longaday said.
“Many survivors have broken bones because they were hit by rocks, logs and debris.”