✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya ta yi kisa tare da lalata amfanin gona na N5bn

’Yan Sanda a Jihar Bauchi sun tabbatar da rasuwar mata biyu da lalacewar gidaje 2,600

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta tabbatar da rasuwar mata biyu da lalacewar gidaje sama da 2,600 da gonaki da dama sakamakon ambaliyar ruwa a Karamar Hukumar Shira ta jihar.

Majiyoyi daga kauyukan da iftila’in ya shafa sun ce wadanda suka mutu sun kai uku, yayin da aka samu rahoton batar wasu da dama a garin Bauchi sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka.

Kakakin Rundunar, DSP Ahmed Mohammed Wakili ya ce ambaliyar ta faru a ranakun Lahadi da Litinin a kauyukan Disina, Bakatma da kuma Adamami.

“Sakamakon ambaliyar, wasu yara mata su biyu masu kimanin shekaru 13 da 19 sun nutse a ruwan, amma daga baya jami’an ceto sun samu nasarar tsamo gawarwakinsu.

“Akalla ambaliyar ta lalata gidaje 2,600 da kuma gonaki da dama a kauyukan”, inji kakakin.

Sai dai ya ce ba su kai ga samun rahoton batar ko da mutum daya ba a garin na Bauchi saboda ruwan saman.

Wani mazaunin kauyen Adamani, Malam Aminu Bala ya ce mutum uku ne suka rasa ransu saboda ambaliyar, yayin da kuma kimanin kaso 85 cikin 100 na gidajen kasa suka rushe da kuma sharewar gonaki da fadinsu ya kai kimanin hekta 3,000.

Ya ce mutanen garin sun shafe tsawon daren ranar ba tare da rintsawa ba a kokarin da suke yi na ceto mata da kananan yaran da baraguzan gini suka danne.

Ambaliyar, a cewarsa ta biyo bayan ruwan da aka tafka na kimanin sa’a 14 daga yammacin ranar Lahadi zuwa Litinin ta kuma shafe kusan ilahirin garin.

Ya kuma koka kan cewa zuwa yanzu kauyen na Adamani da ma wasu sun fuskanci matsalar kusan makonni biyu ba tare da samun kowane irin tallafi daga gwamantin karamar hukuma ko ta jiha ba.

“Mun jima muna kira kan a gina mana hanyar ruwa amma abin mamaki hukumomi sun yi watsi da mu”, inji Malam Aminu.

To sai dai yunkurin jin ta bakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar ya ci tura zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Ambaliyar ta lalata kimanin hekta 500,000 a Kebbi

A jihar Kebbi, Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) Sani Dadodo ya ce kimanin amfanin gona da darajarsu ya kai na Naira biliyan biyar sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar.

Ya ce kimani hekta 500,000 ta gonaki ne ambaliyar ta shafe, wadda daga ciki kimanin 450,000 ta shinkafa ce.

“Darajar abin da aka yi asara a ambaliyar Kebbi ta kai Naira biliyan biyar kuma kimanin kaso 90 cikin 100”, inji shugaban hukumar.

Zuwaira Abubakar, wata manomiyar shinkafa a Karamar Hukumar Argungu ta ce ruwa ya tafi da kusan dukkan gonakin shinkafar yankin, wanda hakan ke nufin sun rasa jarin da za su yi amfani da shi ke nan wajen noman rani.

Zuwaira ta ce takan noma gonakin da fadinsu ya kai fadin hekta 25, wadanda a yanzu ruwa ya tafi da kusan dukkansu.

Ta kuma ce ta kashe sama da Naira dubu 300 a gonar kafin ambaliyar ta tafi da ita.

Daga nan sai ta yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki domin su samu su rage radadin iftila’in.