Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA) ta ce kimanin mutane miliyan 1.6 ne ambaliyar ruwa ta shafa a Najeriya tsakanin watan Afrilu zuwa Satumban 2024.
Darakta-Janar ta NEMA, Hajiya Zubaida Umar ce ta bayyana hakan a yayin wani bikin koyar da dabarun kariya da ɗaukar matakan gaggawa kan ambaliyar ruwa da aka gudana ranar Alhamis a Birnin Kebbi.
- NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024
- Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD
Zubaida wanda Daraktan Rage Haɗarin Ibtila’i na Hukumar, Dokta Daniel Obot ya wakilta, ta kuma ce mutane 634,035 ne suka rasa matsugunansu sannan gidaje 94,741 sun lalace ko kuma sun nutse a ruwa.
Ta ce, dabarun gargaɗin na farko na da nufin haɗe hanyoyin sadarwa kai tsaye da haɗa kai don yaɗa saƙonnin gargaɗi tun farko a matakin jihohi, ƙananan hukumomi da unguwannin.
“Shawarwari na ruwan sama da ambaliya da ke ƙunshe a cikin Hasashen Yanayi na (SCP), da kuma Hasashen Ambaliyar Ruwa na Shekara-Shekara (AFO) na Nijeriya da Hukumar Kula da Yanayi da Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya (NIHSA), duk sun ba mu sanarwar gargaɗi da wuri.
“Saboda haka, dukkanmu ana sa ran za mu ɗauki matakan da za su rage illar da ambaliyar ruwa ka haifarwa ga ɗaukacin ƙasashe da kuma al’ummar Najeriya, musamman ga waɗanda suka fi kowa rauni da ke zaune a cikin unguwannin da ke cikin haɗarin ambaliya,” in ji ta.
Zubaida ta ce, alƙaluman da NEMA ta fitar a ranar 13 ga watan Satumba, sun nuna ƙananan hukumomi 176 a jihohi 30 da suka haɗa da babban birnin tarayya Abuja ambaliyar ruwan ta shafa saɓanin ƙananan hukumomi 148 a jihohi 31 da NIHSA ta yi hasashe.