Basaraken garin Tungbo da ke Karamar Hukumar Sagbama ta Jihar Bayelsa, Amos Poubinafa, yanzu haka ya koma kwana a cikin motarsa sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye fadarsa.
A cewar basaraken, “Mako biyu ke nan na shafe ina kwana a cikin motata kirar Toyota Sienna tun bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye Fadata.
- Ambaliyar ruwa ta raba mutum 400,000 da muhallansu a Kogi
- Dillan miyagun kwayoyi 48 sun fada komar NDLEA a Edo
“Ruwan ya kai har guiwar mutum, wanda hakan ya sa zaman fada ba zai yiwu ba,” inji shi.
Mista Poubinafa, wanda tsohon jami’in sojan ruwan Najeriya ne da ya yi ritaya, ya bayyana hakan ne ga Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a ranar Litinin a Tungbo.
Ya kuma ce, “Motar ita ce kawai wurin da zan iya rabawa don na tsira; duk ginin ya cika da ruwa makil kuma babu wani waje da zan iya kwana face cikin motar.
“Na kwashe iyalaina zuwa Yenagoa. A matsayina na Kyaftin din soja kuma basaraken gargajiya, ba zan iya barin talakawana na tafi wani waje neman mafaka ba.
“A matsayina na wanda ya samu horon sojan ruwa, ba zan bar tawagata ba, zan tsaya kai da fata har komai ya daidaita,” a cewarsa.
Mista Poubinafa ya kuma shaida wa NAN cewa shi ma ya sha fama da ambaliyar ruwa a shekarar 2012 saboda ba zai iya barin mutanensa ya koma wani matsuguni ba, amma ya ce lamarin na yanzu ya yi muni sosai.
Ya yi kira ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da takwararta ta Jihar Bayelsa, da sauran masu hannu da shuni da su taimaka wa wadanda ambaliyar ta shafa a garin na Tungbo.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gina madatsun ruwa da za su ratsa kogunan Neja da Binuwai domin kawo karshen ambaliyar ruwa a sassan kasar nan.
Mista Poubinafa dai ya yi ritaya daga aikin sojan ruwan Najeriya a matsayin Babban Kwamanda a shekarar 2002, kafin daga bisani ya zama basaraken gargajiya a yankinsa.