Ambaliyar ruwa ta mamaye wani rukunin gidaje da aka gina a kusa da wani rafi a garin Deidei, Abuja inda ta yi sanadiyyar mutuwar mata biyu da yaro dan shekara hudu.
Ruwan wanda aka fara da misalin karfe 10:00 na dare a ranar Litinin da ta gabata ya dauke ne bayan awa biyu, inda ya rusa gine-ginen da ke kusa da rafin da wasu a nesa bayan rafin, ya mamaye yankin, kamar yadda wani da ruwan ya rusa wa gida mai suna Malam Yunusa Muhammed, ya bayyana wa Aminiya.
Mahaifin matan biyu da suka rasu mai suna Malam Yakubu Abdussalam wanda masanin tattalin muhalli ne, ya ce ya shekara 16 da gina gida ba tare da fuskantar ambaliyar ba. Ya ce an sanar da shi faruwar lamarin ne lokacin da yake garinsu Okene inda aka shaida masa cewa ’yarsa mai suna Ramatu mai shekara 30 da Maryam mai shekara 26 da jikansa mai suna Yusuf dan shekara 4 sun rasu saboda sun kasa fita daga gidan lokacin da ambaliyar ta rutsa da su a gidan, wanda ke gabar rafin da aka yi masa kariya da itatuwa da shuke-shuke.
Ya ce sauran ’ya’yansa da ke gidan Abubakar da Abdullahi sun kubuta daga lamarin. Kuma ya ce ya yanke shawarar gina gida a wurin ne sakamakon sha’awar da yake da ita kan sana’arsa ta tattalin muhalli yin shuke-shuke.
Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello ya ziyarcin yankin tare da Shugaban karamar Hukumar Bwari, Mista Musa Dikko inda Ministan ya jajanta musu, kuma ya umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Birnin Tarayya (FEMA) ta agaza wadanda matsalar ta shafa.