Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar mamaye gidaje sama da 150 da gonaki masu dimbin yawa a garin Kuri da ke yankin Karamar Hukumar Yamaltu-Deba a Jihar Gombe.
Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin, Ahmad Muhammad Sa’ad, shi ne ya bayyana hakan a madadin al’ummar garin a lokacin da suka fito don gudanar da aikin gayya dan tone hanyar da ruwa zai wuce.
Ya ce sun yanke shawarar yin aikin ne don ragewa kan su matsalar ambaliyar a nan gaba.
A cewar sa al’ummar, sun yi iya bakin kokarinsu wajen gyara hanyoyin ruwa amma hakan ba zai wadatar ba sai dai ya rage saboda aikin yafi karfin su, dole sai gwamnati ta shigo ciki.
Muhammad Sa’ad, ya ci gaba da cewa ambaliyar ta jawo musu asarar dukiyoyi da amfanin gona masu yawa.
Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin Jihar Gombe da ’yan Majalisar dake wakiltar yankin a matakin Jiha da tarayya da ma sauran shugabannin al’umma da su kawo musu dauki.
Da yake zantawa da manema labarai, Babban Limamin garin na Kuri Malam Adamu Muhammad, ya bayyana cewa makasudin wannan aikin gayyar shi ne don su samar da magudanun ruwan da ruwan nan gaba ruwan da zai rika wucewa cikin sauki,
Daga nan shi ma ya yi roko ga hukumomin da abun ya shafa da su yi dukkan mai yuwuwa dan ceto gidajen su da gonakin daga ambaliya.
Mazauna garin dai sun kira ga gwamnati da ta kai musu daukin gaggawa ta hanyar gina musu hanyar ruwa don gujewa wata asarar a nan gaba.