Dan Majalisar Tarayya na Bade/Jakusko a Jihar Yobe, Zakari Ya’u Galadima, ya ce ambaliyar ruwa ta mamaye kusan illahirin mazabarsa.
Ya’u Galadima ya ce ambaliyar ta shafi ko’ina a Bade da Jakusko da ke iyaka da jihohin Jigawa da Bauchi.
- ’Yan bindiga sun sace dan kasuwa da dansa a Jalingo
- Mata 800,000 na fama da Yoyon Fitsari a Najeriya —UNFPA
Dan majalisar ya bayyana cewa a matakin Majalisar Dokoki ta Kasa sun yi ganawa da wasu ’yan majalisar da suka fito daga wasu jihohi da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan inda suka fito da wata takarda wadda suka mikawa majalisar ta hannun Shugaban Majalisar Dattawa.
Ya ce za a mika takardun zuwa ga hukumomin gwamnati da ma’aikatun da abin ya shafa kamar su ma’aikatar noma ta tarayya, ma’aikatar jin kai da ma’aikatar kula da bala’o’i da ma’aikatar lafiya domin su shirya tunkarar lamarin.
Dan majalisar ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya kiyaye afkuwar irin wannan bala’i a nan gaba, Ya kuma bai wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu ikon jure wannan rashin.
Alhaji Ya’u Galadima ya kuma jajanta Wa mutanen da ambaliyar ta rutsa da gonake da muhallinsu.