Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 51 tare da lalata gidaje 26,000 a cikin wata biyu a Jamhuriyar Nijar.
Gwamnatin kasar ta ce ambaliyar ta shafi mutum 281,000 daga iyalai 32,500, a cikin watan Yuli da Agusta.
Shugaba Mahamadou Issoufou ya shaida wa taron gaggawar da gwamatinsa ta kira cewa ruwan da ya yi ambaliya daga Kokin Neja ya shafe hekta 5,500 na amfanin gona.
Jamhuriyar Nijar na tsakiyar damunanta da ke kamawa daga watan Mayu zuwa Oktoba, inda ruwan saman ya fi karfi a watannin Yuli da Agusta.
Kasar na yawan fama da amabliya inda ruwan sama mai karfi ke yin sanadiyyar mace-mace ko raba mutane da matsugunansu sakamakon rashin ingatattun ababen more rayuwa.