Sakamakon ruwan da ake tafkawa a Jihar Adamawa, an samu ambaliyar ruwa da dama a bangarori daban-daban na jihar wadda ta ci akalla gidaje 300.
Ambaliyar ta fi aukuwa ne sakamakon ruwan da aka yi daga ranar Litinin zuwa Talata.
Bangarorin da ambaliyar ta fi shafa su ne bayan unguwar Kamfanin PZ da Damilu da Wuro Jabbe a Karamar Hukumar Yola ta Arewa da kuma Unguwan Jambutu.
Sannan akwai wasu wurare kamar su Unguwar Bachure da Saminaka da Ngurore da hanyar Barikin Soji.
Koda yake babu wanda ya rasa ransa sakamakon ambaliyar, amma an rasa dukiyoyi da akalla za su kai miliyoyin Naira ciki har da kayan abinci.
Wani mazaunin Yola, Malam Shehu Modibbo ya ce, “Idan har hanyoyin da Gwamnan Jihar ke yi ba za su iya magance wannan matsala ta ambaliya ba akwai damuwa.”