✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya na ci gaba da kassara Arewa

Ambaliyar ta fi yin ɓarna a jihohin Jigawa da Bauchi da Sakkwato da Kano da Yobe

Ambaliyar ruwa tana ci gaba da kassara jihohin Arewa a daminar bana duk da gargaɗin da hukumomi suka riƙa yi kafin aukuwarta.

Ambaliyar ta fi yin ɓarna a jihohin Jigawa da Bauchi da Sakkwato da Kano da Yobe, waɗanda suke cikin jihohi 31 da Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta ce za su haɗu da ambaliyar a bana.

Jihar Jigawa ce kan gaba wajen asarar rayuka inda aka samu rahoton rasuwar mutum 50.

Ministan Tsaro Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya bayyana wa Gwamnan Jihar cewa sun samu rahoton rasuwar mutum 33 a ambaliyar tare da lalata gidaje da gonaki a ƙauyuka 148 a ƙananan hukumomi 14 na jihar.

Minista Badaru ya bayyana haka ne, lokacin da ya ziyarci Gwamna Umar Namadi a Dutse inda ya ce ambaliyar ta shafi sama da mutum dubu 50 tare da illa ga gonaki dubu 11 da 500.

Jihar Jigawa wadda ke cikin jihohin da suke fuskantar amabliya a kowace shekara lamarin ya fi muni a bana kamar yadda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ta bayyana.

Shugaban Hukumar SEMA, Alhaji Yusuf Sani, ya ce sun samu rahoton rasuwar mutum 50 a ambaliyar da ta auku a ƙananan hukumomin jihar 27, inda ya ce an tura ma’aikatan jin ƙai zuwa yankunan da ambaliyar ta auku don ƙirga waɗanda ambaliyar ta shafa inda ya ce sun kai dubbai.

Ya ce, Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa ce ambaliyar ta fi yi wa illa inda ta hallaka mutum 10, aka kwantar da 68 a asibiti, yayin da ta raba mutum 1,436 da muhallansu – akasari a ƙauyen Balangu inda ta lalata gidaje 237.

Sannan mutanen jihar suna zaman ɗar­ɗar kan yiwuwar samun ambaliyar daga Kogin Komadugu da kuma yiwuwar cika da tumbatsar madatsun ruwa na Tiga da Chalawa a Jihar Kano, wanda hakan na iya shafar Jihar Jigawa kamar yadda ake samu duk shekara.

A Jihar Bauchi ambaliyar ta auku a ƙananan hukumomi 12 daga cikin 20 da take su, inda ta jawo asarar rayuka da dukiya da lalacewar hanyoyi da gadoji da gonaki da gidaje.

Babban Daraktan Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Bauchi (BASEPA), Alhaji Mas’ud Aliyu ya ce manyan tituna biyar sun lalace dalilin ambaliyar.

Ya ce daga cikinsu hanyar Kano daga Azare zuwa Jama’are gada ta yanke, haka hanyar Giyaɗe zuwa Azare ta yanke.

Sai hanyar Shira zuwa Azare ita ma ta yanke, hanyar Udubo zuwa Gamawa ma ta yanke sannan Kogin Illalla ya malala a Ƙaramar Hukumar Zaki har ya yanke hanyar Zindiwa.

Alhaji Mas’ud Aliyu ya ce ƙananan hukumomin da ambaliyar ta fi yi wa illa su neKirfi, Bauchi, Katagum, Zaki, Gamawa, Ningi, Warji, Kirfi, Tafawa Ɓalewa, Toro, Darazo da Ganjuwa.

Ko’odinetan Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Bauchi (SEMA), Dokta Abubakar Umar Gabarin ya ce an samu ambaliyar ruwa a kusan kowane ɓangare na jihar.

Ya ce a garin Cheledi a Ƙaramar Hukumar Kirfi, ambaliyar ya shafe da gidaje da gonaki 280, sai garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro inda ambaliyar ta lalata gidaje da gonaki 148.

Sai garin Kari a Ƙaramar Hukumar Darazo ta yi ɓarna a gidaje da gonaki 67, sai kuma garin Zindi a Ƙaramar Hukumar Misau inda ta lalata gidaje da gonaki 85.

Garin Gaɗiya a ƙaramar Hukumar Gamawa kusan kashi 80 ambaliyar ta lalata.

Ya ce ambaliyar ta shafe fiye da gidaje 200 da gonaki sama da 300, a Gamawa sai garin Buskuri da ke Ƙaramar Hukumar Katagum gada ta yanke ba a shiga garin kuma ruwa ya mamaye garin ya kuma tafi da gonaki.

Haka hanyar Bulkachuwa ma ruwan ya lalata ta.

Sauran ƙananan hukumomin da ruwan ya tafi da gidaje da ɗaruruwan gonaki sun haɗa da Zaki, Giyaɗe, Shira, Jama’are da Bauchi.

Jami’an Hukumar SEMA sun ce, ambaliya ta raba mutane da dama da matsuguninsu yayin da manoman suka yi asara mai yawa saboda shafe gonarsu da ruwan ya yi.

Dokta Abubakar Gabarin ya ɗora alhakin munin lamarin kan yadda jama’a suka yi biris da gargaɗin da Hukumar NiMet ta yi don kauce wa ambaliyar duk da ta ba da sunayen wuraren da za a yi ambaliyar.

“Abin takaici, jama’a ba su kula ba, har ambaliyar ta fara aukuwa a sassan ƙasar nan, ciki har da jiharmu.

“A nan Jihar Bauchi mun yi tarurrukan wayar da kan masu ruwa- da-tsaki da wakilan al’ummar da ake sa ran ambaliyar za ta shafa.

“Ita ma Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta yi irin wannan taro.

“Kuma an ci gaba da hakan ta kafofin yaɗa labarai amma mutane ba su kiyaye ba,” in ji shi.

Dokta Gabarin ya ce gwamnatin jihar za ta gudanar da aikin tantance ɓarnar da aka yi da nufin bayar da agaji don rage raɗaɗi ga mutanen da abin ya shafa.

Ya ce kamar a Ƙaramar Hukumar Kirfi ayarin ƙwararru da suka haɗa da injiniyoyi daga ma’aikatun albarkatun ruwa, ayyuka, filaye da safiyo, jami’an SEMA da Hukumar Raya Arewa maso Gabas sun ziyarci yankin da nufin tantance matsalar da kuma samo hanyar da ta fi dacewa a magance ta.

Ya ce sun samu labarin cewa ambaliyar ta fito ne daga wajen garin, kuma ƙwararru na iya karkatar da hanyar da ruwan ke bi ya shiga garin.

Sannan ana tantance sauran wuraren da abin ya shafa don a ƙididdige abin da ya faru.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi SP Muhammed Ahmed Wakil ya tabbatar da cewa kwale-kwale ya kife da mutum biyar kuma an ceto uku, biyu kuma ba a same su ba.

A garin Nahutan Taba da ke Ƙaramar Hukumar Toro mazaunansa sun ce kwale­kwalen ya kife da mutun bakwai amma duka sun tsira, sai dai ruwa ya tafi da saniya da babur.

Jami’an Hukumar SEMA da ’yan sandan jihar sun tabbatar da kifewar kwale- kwalen amma sun gaza tabbatar da yadda abin ya faru da yawan asarar da aka yi na rai ko dukiya.

Amma Alhaji Mas’ud Aliyu ya tabbatar da rasuwar mutum uku a Giyaɗe.

Kuma akwai rahotannin da ke cewa wasu mutum takwas sun rasu a ambaliyar inda adadin waɗanda ake zaton sun rasu ya kai mutum 18 a jihar.

Wasu mazauna garin Kirfi sun buƙaci gwamnati ta samar musu da wani matsuguni ta ɗage su daga yankin saboda ambaliyar ruwan tana faruwa a kowace shekara tsawon shekara biyar.

Da take bayyana halin da suke ciki a garin Gaɗiya da ke Ƙaramar Hukumar Gamawa, Hajiya Amina Gaɗiya, ta ce ambaliyar ta lalata kusan rabin garin saboda yawancin gidajensu na ƙasa ne.

Ta ce gonaki da dama ruwa ya tafi da su. Sai ta yi kira ga gwamnati ta kula da su a Gaɗiya da kewaye, ta ce suna fuskantar matsalar rashin abinci da tufafi da wurin kwana.

Sarkin Gaɗiya Alhaji Ya’u Umar ya ce sama da mutum 100 ne ke zaman mafaka a fadarsa kuma ɗaruruwan mutane suna zaune a masallatai da makarantu a matsayin mafaka na wucin­gadi.

Ya ce sama da mutum 200 sun rasa matsugunansu kuma sama da gonaki 300 ne ambaliyar ta rutsa da su.

Hakimin Gamawa Alhaji Abdulƙadir ya ce ambaliyar ta tasam ma cinye garin Gamawa sai da suka yi ta yin aikin gayya suna toshe hanyoyin da ruwan ke kwarara.

Tuni gwamnatin jihar ta kai kayayyakin agaji ga mutanen Kirfi, Gamawa, Bauchi, Zaki, Misau, Shira, Giyaɗe da Katagum.

Haka Sanata Shehu Buba da ke wakiltar Bauchi ta Kudu ma ya aika da kayayyakin abinci yayin da Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Ambasada Yusuf Tuggar ya ba su Naira miliyan 20.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tura Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi ya je ya jajanta wa mutanen yankunan da ambaliyar ta shafa kuma ya yi alƙawarin gyara hanyar da gadar ta yanke.

A Jihar Sakkwato kuwa ambaliyar ta lalata gidaje 14,940 kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar.

Shugaban Kwamitin Kula da Ambaliya na Jihar, Alhaji Muhammad Bello Idris ya sanar da haka a lokacin da yake gabatar da rahoton kwamiti ga Gwamnan Jihar Alhaji Ahmad Aliyu a ranar Litinin da ta gabata.

Ya ce ƙauyuka 1,341 a ƙananan hukumomi 22 ne lamarin ya shafa a wannan shekarar.

Ya ce gonaki 11,390 ne suka lalace. Kwamitin a rahotonsa ya yi kira ga gwamnati ta ba da agajin gaggawa ga waɗanda lamarin ya shafa.

Gwamnan ya gode wa kwamitin tare da ba da tabbacin aiwatar da rahoton kwamitin a tsanake.

Ambaliyar ta mamaye ƙananan hukumomi takwas da suka haɗa da Gwaronyo da Sabon Birni da Illela da Silame da Binji da Gada da Kebbe da Shagari, inda mutane masu yawa suka daina kwana a gidajensu sanadiyar ambaliyar.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Illela Alhaji Sahabi Wakili ya ce ambaliyar ta tayar da gidaje sama da 300 a ƙaramar hukumar.

Shugaban ya nemi gwamnatin jihar ta taimaka wa mutanen da ambaliyar ta shafa domin suna fuskantar wahalar wurin zama, wasu na laɓe a gine-ginen gwamnati a takure saboda wurin ya yi musu kaɗan, yayin da wasu suke zaune a cikin kangayen gidaje.

A Ƙaramar Hukumar Gwaronyo, Malam Kabiru Gwaronyo ya ce “Ambaliyar ta ɓarnata kayan gona masu yawa, shinkafar ta lalace, ko’ina ruwa ya mamaye gonakinmu.”

Ya ce dole ne a samu ambliya a Gwaronyo domin gulbin yankin ya cushe ko ruwa ya zo ba ya tsayawa yashi ya yi yawa.

Ya ce matuƙar gwamnati ba ta yi wani abu kan gulbin ba dole kowace shekara a samu ambaliya.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ya ce ba zai ce komai kan lamarin ba, sai an ba shi izini, in ya samu amincewa zai yi magana kan ambaliyar, sai dai har zuwa haɗa wannan rahoton bai waiwayi wakilinmu ba.