An samu mummunan ambaliyar ruwa a yankuna da dama a ƙaramar hukumar Madagali ta Jihar Adamawa, inda ta jawo salwantar rayuka da asarar dukiya mai tarin yawa.
Rahotanni sun bayyana cewar ambaliyar ta yi ajalin mutum shida, ta raba sama da mutum 2,000 da gidajensu, tare da lalata gonaki, da gadoji masu yawa.
- An soma biyan ma’aikata sabon albashi mafi ƙaranci a Adamawa
- Ambaliya: NEMA ta nemi jama’a su share magudanun ruwa a Edo
Wuraren da ambaliyar ta fi shafa sun haɗa da Kichinga, garin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, tare da Mildu, Maradi, Mayo Wandu, Shuware, Pambla 2 da Palam.
Shugaban ƙaramar hukumar Madagali, Hon.Simon Musa, ya tabbatar da afkuwar ambaliyar a wata hira da ‘yan jarida.
Ya bayyana cewa ambaliyar ruwan ta bana ta shafi wuraren da ba su taɓa fuskantar matsalar ba a baya.
Ya ce dubban mutane da ambaliyar ta raba da gidajensu yanzu haka suna zaune a sansani 10 na wucin gadi da aka kafa don taimaka musu.
Musa, ya ce ambaliyar ta faru ne sakamakon mamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka tafka a kan Dutsen Mandara, wanda ya haifar da zaizayar ƙasa da lalata Gadar Shuwa, gidaje, kayan abinci, da gonaki.
Ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta jihar, da kuma ƙungiyoyin agaji, su kai wa yankunan ɗauki cikin gaggawa.
Hakimin Shuwa, Mustafa Mohammed Sanusi, ya bayyana lamarin da “abun tausayi.”
Ya roƙi gwamnatin jihar da ra gaggauta taimaka wa yankunan da ambaliyar ruwan ta ɗaiɗaita.