✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Manoman Kaduna sun sami tallafin Gwamnatin Tarayya

Manoma 210 ne suka samu gajiyar tallafin irin shuka a jihar.

Gwamnatin Tarayya ta ba wa manoma 210 da ambaliya ta shafa a Jihar Kaduna tallafin irin shuka don rage musu radadin da suka shiga.

Mataimakiyar Darakta a Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya,  Misis Omotosho Agbani, ta ce tallafin wani shiri ne na taimakon manoman da ambaliya ta shafa a 2022 da sabbin kayan aikin noma.

“Muna son manoma su yi amfani da wannan tallafi don habaka nomansu,” in ji ta, a lokacin da take rabon kayan a Kaduna.

A cewarta, kayayyakin sun hada da irin tumatir, albasa, kayan lambu, ’ya’yan itatuwa da sauransu.

Agbani ta ce an yi rabon kayayyakin ne a lokaci guda a jihohin Kano, Gombe, Adamawa, Edo, Delta, Bayelsa, Anambra, Kogi Benuwai, Ogun da Oyo.

Ta ce ambaliyar 2022 ta haifar da damuwa ga manoma tare da raba mutum miliyan 1.4 da muhallansu a fadin Najeriya.

Ta kara da cewa, baya ga mace-mace da asarar gidaje da ababen more rayuwa da aka samu, ambaliyar ta shafi gonaki 332,327.

Dokta Timkat Vontau, daraktan aikin gona na tarayya a jihar, ya ce gwamnati ta yanke shawarar samar da “muhimman bayanai cikin sauri” don taimaka wa wadanda abin ya shafa su koma gonakinsu da aiki.

Ya ce ambaliyar ruwan ta yi barna, don haka ya zama wajibi Gwamnatin Tarayya ta rage wa mutane radadin da suke ciki.

Mohammed Sa’id, ma’aikaci a Hukumar Raya Aikin Gona ta Jihar Kaduna, ya ce gwamnatin jihar na sabunta bayanan manoma a fadin jihar.

Ya kuma ja hankalin wadanda suka amfana da su yi amfani da kayayyakin da aka ba su, inda ya ce jihar na fatan samun karin tallafi daga Gwamnatin Tarayya.

Mohammed Ismail wanda ya yi magana a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, ya yaba wa gwamnatin  bisa wannan karimci da aka musu.