Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da Hukumar Raya Arewa Maso Gabas (NEDC) da sauran hukumomi su taimaka wa al’ummar garin Darazo na Jihar Bauchi da ambaliyar ruwa ta shafa a kwanakin baya.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Darazo/Ganjuwa, Mansur Manu Soro, ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.
Dan majalisar ya ce ambaliyar ta garin Darazo na Karamar Hukumar Darazo ta lalata gidaje sama da 200 da gonaki da sauran kayan amfani.
Soro ya kuma bukaci a ci gaba da aikin kula da zaizayar kasa da inganta hanyoyin da Ofishin Asusun Kula da Muhalli ke aiwatarwa domin magance yawaitar ambaliyar ruwa a Darazo.
Ya nuna damuwarsa da halin da dubban ’yan Najeriya ke ciki sakamakon bala’in ambaliyar a garin na Darazo.
Don haka majalisar ta bukaci Hukumar NEMA da ta tallafa wa wadanda iftila’i ya shafa.
Ta kuma bukaci NEMA da hukumar NEDC su hada hannu da Gwamnatin Jihar Bauchi da nufin sake taimakon al’ummar Darazo wadanda ambaliyar ruwan ta raba da muhallansu.
Majalisar ta zartar da kudirin ne bayan wata kuri’ar da Mataimakin Shugabanta, Ahmed Idris Wase, ya jagoranta.