Akalla iyalai 120 ne suka rasa muhallansu a Unguwar Tsallake ta Karamar Hukumar Guri a Jihar Jigawa, sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliya.
Jami’in yada labaran yankin, Sunusi Doro, ya sanar a ranar Asabar cewa lamarin ya faru ne bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a ranakun Laraba da Alhamis.
Doro ya ce ambaliyar ta mamaye gidaje sama da 120, wanda hakan ya sa mutanen da ke cikin gidajen rasa matsuguni a halin yanzu.
“Wasu daga cikin gidajen sun riga sun rushe yayin da wasu suka nutse a ruwa.
“Mafi yawan wadanda lamarin ya shafa sun koma da zama a gidajen danginsu, saboda ruwa ya hana su shiga nasu gidajensu,” inji Doro.
Ya yi bayanin cewa ambaliyar ta datse hanyar zuwa babban asibitin yankin, wanda dama can sai sun bi ta ruwan kafin su samu damar zuwa asibitin.
Shugaban Karamar Hukumar, Musa Shuaibu, ya tausaya wa wadanda abin ya shafa, inda ya yi kira ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da su kawo musu dauki.
Shuaibu ya ce a matakinta ta samar da buhuna ga mazauna yankin don fara sanya jinga domin dakile ambaliyar ruwan.
Kazalika, ya shawarci mazauna yankin da su rika share kwalbatoci da magudanan ruwa domin tabbatar da tsaftataccen muhalli, wanda hakan zai ba wa ruwan sama damar wucewa.
“Shugaban ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba majalisar za ta sayi kayayyakin agaji don rabawa ga wadanda suka kamu da cutar kwalara a yankin.
“Ya ce zuwa yanzu majalisar ta kashe N400,000 wajen sayen magunguna ga kauyuka bakwai da aka samu barkewar cutar,” inji Doro.