Hukumar Ci gaban Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) da hadin gwiwar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (SEMA) sun tallafa wa al’ummar garin Damaturu da suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwa a kwanakin baya domin rage musu radadin da suke fuskanta.
Jami’in hukumar NEDC a Jihar Yobe, Dokta Ibrahim Abbas, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a lokacin kaddamar da rabon kayan tallafin a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
- An sako matar da ta kashe mijinta a Kano daga gidan yari
- An yi garkuwa da Sakataren Hukumar Zabe a Nasarawa
Ya jinjina wa masu ruwa da tsaki na NEDC da SEMA da ke garin Damaturu da ‘yan sa kai har ma da wadanda suka samu tallafin bisa hadin kai da suka basu wajen rabon kayan cikin tsanaki.
Abbas, ya kuma bayar da tabbacin cewa za su ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsakin da sauran hukumomi don cimma kudurin NEDC a jihar Yobe.
“Wannan hadin gwiwar zai ci gaba da dorewa don cimma nasara, zaman lafiya da ciyar da jihar Yobe gaba.”
Wasu da suka samu tallafin sun bayyana jin dadinsu ga hukumomin biyu na NEDC da SEMA ta yadda aka tuna da su aka ba su tallafi don rage musu kuncin rayuwa da suka shiga sakamakon ambaliyar ruwa da ta yi musu barna.
Sun kuma gode wa gwamnatin jihar Yobe kan yadda take bayar da taimako cikin gaggawa ga al’ummar da suka shiga mawuyacin hali sakamakon iftila’in ambaliyar ruwa ko gobara.