✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amarya ta rataye kanta a Zariya saboda auren dole

Ta dauki matakin ne bayan an aura mata mijin da ba ta so

Al’ummar unguwar Tudun Muntsira da ke Cikaji a Karamar Hukumar Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna sun cika da alhinin yadda wata amarya ta rataye kanta a unguwar.

A ranar Juma’a 29 ga watan Afirilun 2022 da misalin karfe 6.:00 na yamma ne dai labari ya cika unguwar cewar wata matar aure mai suna Sanayya Muhammad nai shekara 16 da a unguwar ta kashe kanta ta hanyar rataya.

Bayanan da Aminiya ta samu shi ne wai an daura mata aure ne da angon nata mai suna Isa Jibrin mai shekara 35 wanda ta ce sam ba ta son shi.

Amaryar dai ’yar asalin garin Nasarawan Doya ce da ke Karamar Hukumar Makarfi da ke Jihar ta Kaduna.

Wani jami’in dan sanda wanda da shi ne aka je inda amaryar ta rataye kanta ya ce sun tarar da ita a mace.

Kazalika, ya ce sun same ta a wani yanayi mara kyan gani, inda nan take suka dauki gawar suka kai ta asibiti domin fadada bincike.