Wata amarya da aka yi bikinta watanni uku da suka wuce a unguwar Hammadu Kafi a garin Gombe, mai suna Zainab Haruna, mai kimanin shekaru ashirin da biyu, ta kwakule idon kishiyarta uwargida, mai suna Hadiza Musa Hammadu, mai kimanin shekaru talatin, a wani gumurzu da suka yi kwanan baya.
Aminiya ta je gidan Alhaji Musa Hammadu, mahaifin Hadiza, don jin yadda al’amarin ya faru.
Yayin da take bayani, Hadiza Musa, wadda ta rasa ido daya, ta ce, “Mun jima muna zaune da mijina, sai ya yi min kishiya, kimanin watanin uku da suka gabata kuma tun da aka kawo ta gidan, muna zaman lafiya da ita. Ba ta taba nuna min wani mugun hali ba. Sai ranar Litinin 28 ga watan jiya (Afrilu), bayan mun ci abincin rana mun gama, sai na shiga daki, na bar ta da ’ya’yana biyu da kuma wata ’yar budurwa ’yar wan maigidanmu. Sai ta ce min tana son yaran nan su tafi unguwa, su bar gidan ko su je gidan makwabta, sai na ce mata tunda suna zuwa makarantar Islamiyya idan sun dawo daga boko, ta bari sai ranar da babu Islamiyya, kamar ranar Alhamis ko Juma’a, sai su je, sai ta ki. Ta matsa sai sun je unguwar. Ganin kar ta ce ina hana yarana abin da ita take so, sai na ce to, su je. Ita ’yar budurwar kuma ta ce da ma an bar zuwa unguwar, tunda ita ba ta jin dadi. Ganin amaryar ta matsa ne, kawai sai na ce su je.
“Ni dai ban kawo komai a raina ba, ganin yadda muke zaune lafiya tunda ta shigo gidan, domin ko baki muka yi suna ce mana muna zaman lafiya. Ashe akwai abin da take shiryawa a zuciyarta, ban sani ba. Yaran suna fita sai ga wata mata ta shigo, wadda, ni ban san ta, bakuwarta ce ’yar unguwarsu mai suna Ummi, kuma ba ta wuce minti biyar ba ta fita.
“Bakuwa na fita, sai na tafi daki don in yi wanka, in yi sallar Azahar. Kasancewar bandakina yana cikin dakina, ina fitowa daga wanka, sai na ga Zainab a bakin gadona, na ce, ‘Lafiya na gan ki a cikin dakina?’ Ba ta ce min komai ba, sai kawai na ji ta watsa min wani abu a fuskata, nan take na fara jin hajijiya. Sai ta kamo wuyana ta shake ni, ina ce mata, ‘Lafiya Zainab, me na yi miki?’ Sai na fadi, ita kuwa sai ta dinga tura min hannayenta a cikin idona tana kokarin kwakulewa. Ina ta kokarin kwacewa, ina daga kwance a kasa, sai na fara kururuwar, ‘Jama’a ku zo ku taimake ni’, amma babu wanda zai ji ni da yake gidan yana da zurfi kuma ta kulle gidan. Kuma da ma ashe ta shigo dakin da tabarya, sai ta dauko ta kwada min a kai, sai hancina da bakina suka fara zubar jini.
“Sai kuma ta hau kaina tana ta shake ni tana kokarin cire min ido, ina ta ce mata, ‘Me na yi miki ne Zainab, ki yi hakuri, idan miji ne ki je ni na bar miki’. Shi ne ta ce min ba ina sallar dare da yin addu’a ba, kuma wai idan mijinmu yana dakina ina yi masa magana a kanta. Sai na ce mata, ‘Idan haka ne ki bari, idan ya dawo a tambaye shi’.
“Da Allah Ya taimake ni, sai na kama yatsarta na ciza na kuma rike rigarta, amma duk da haka ba ta sake ni ba. Cizon da na yi mata ne ya sa har na iya jan jikina zuwa falona, ina ta ihun neman taimako. Shi ne ta ce idan ina so ta rabu da ni, in daina ihu, in ba haka ba kuma za ta kashe ni. Ina kusa da fita daga falon nawa, sai ta ga kettle dina, ta dauko ta sake doka min a kai. Ta ce min in yi addu’ata ta karshe, domin yau kashe ni za ta yi, amma kafin ta kashe ni, idan ina addu’ar dare me nake cewa? A lokacin ne ta karasa zakulo min idona waje. Ina jin azaba, sai na ce mata, ‘Ai ko yanzu kika bar ni kin kashe ni domin ba na gani’.
“Ashe kafin ta shiga dakin nawa ta dauko turmina ta ajiye, sai ta dauko shi ta doka min a kaina, har sau biyu, ka ga wajen ma. Sannan ta sake jawo gashin kaina ta buga a jikin turmin. Tana cikin dukana, sai ta ji karar mota, ashe maigidanmu ne ya dawo. Tana lekawa ta gan shi, sai ta sa ihu tana cewa, ‘Wayyo Allah, ka zo ka taimake ni, za ta kashe ni’. Sai na ce mata, ‘Ashe ba ki tsoron Allah! Za ki kashe ni, kuma kina cewa ni ce zan kashe ki?’ Sai na ji yana ta jijjiga kofa, ina cewa, ‘Ka yi sauri, za ta karasa ni. Ka hauro ta katanga’, ita kuma tana cewa wai ya zo ta taga, amma duk da haka ban sake ta ba. A tunanina, kafin ta bude masa kofa za ta iya kashe ni, tunda na ji ta ce za ta dauko kananzir ta kona ni ko ta dauko wuka da burma min, in ya so in ta karasa ni sai ta je ta bude masa kofa. “A hakan ina ta jan jikina da muka zo kusa da kofa, sai na hankada ta. Tana bude kofar sai ta fadi gefena tana cewa, ‘Innalillahi wa’innailaihi raji’un’. Maigidanmu ya shigo a kidime ya ce bari ya nemo jama’a su taimaka, sai na ce masa, a’a, kar ya fita, ya dauke ni a haka, domin in ya fita za ta kashe ni. Shi ne ya nemo zani ya daura min da hijabi, aka kai ni asibiti”.
Mahaifin Hadiza, Alhaji Musa Hammadu, ya shaida wa Aminiya cewa yayin da ya ji labarin halin da ’yarsa take ciki, kuma ya je ya ganta, yanke jiki ya yi ya fadi, sai dawowa da shi gida aka yi. “’Yata mai hakuri ce a cikin ’ya’yana, kuma ba ta son tashin hankali. Duk shekarun da ta yi a gidan mijinta, ba a taba kawo min kashedinta ba. Ita da amaryarta sun zo nan gida sun gaishe ni. Fatana kawai hukuma ta duba irin raunin da aka yi mata, a bi mata kadinsa”. Inji shi.
Lauyan masu kara, Barista Abdullahi Muhammad Inuwa, cewa ya yi a matsayinsa kuma mamba a kungiyar kare hakkin bil Adama, zai tsaya sosai wajen ganin an kwato wa Hadiza Musa hakkinta, musamman ganin kafarta daya ba ta da lafiya tun tana karama, lamarin da ya sa amarya ta samu dama ta dinga tumurmusa ta har ta yi mata wannan mummunan rauni na kwakwale mata ido.
Barista Abdullahi Inuwa, ya ce likitoci sun bayyana cewa wannan ido nata zai yi wuya ya sake gani, amma da aka kai wadda ake tuhuma wajen ’yan sanda a ofishinsu na Pantami, wanda laifin da ta aikata yunkurin kisan kai ne, amma suka ba da belinta.
Ya ce, “Ganin haka ya sa muka nuna rashin jin dadinmu, a kungiyance, muka rubuta takardar korafi wajen kwamishinan ’yan sanda, sai aka sake kama ta, kuma maimakon a tuhume ta a kan yunkurin kisan kai, sai suka tuhume ta da laifin jin rauni. Nan ma muka sake rubuta koke ga kwamishinan ’yan sanda da kwamishinan shari’a na jiha, shi ne aka tura mu kotu.
Wakilinmu ya yi kokarin ganawa da amarya Zainab don jin ta bakinta, amma hakan ya ci tura, domin tana tsare a gidan yari tana zaman jiran shari’a.
A lokacin da aka shiga kotu ranar Talata, aka karanta wa Zainab Haruna tuhumar da ’yan sanda suke mata, sai ta musa aikata hakan ba. A nan ne kuma alkalin kotun Majistare ta 7, inda ake shari’ar, Mai Shari’a Bello Sharif, ya nemi su saurara zai gana da su a cikin ofishinsa don neman yi musu sulhu, lamarin da ya sa Barista Abdullahi ya ce shi bai zai tsaya ba, domin ba sulhu ya kamata a yi ba, kadin wacce aka yi wa illa ya kamata a bi.
Da wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar ’yan sandan jihar, DSP Fwaji Atajiri, ya ce suna sane da wannan al’amarin, amma kuma shi lauyan masu karar da ya ce yana ganin ba a yi wa ita mai laifin cajin da ya kamata ba, ai magana zai yi don a gyara, tun kafin shari’a ta yi nisa, tunda shi masanin shari’a ne, ba shiru zai yi ba don gudun kada sai an yanke hukunci ya ce ba a kyauta masa ba.
A halin yanzu dai an dage karar sai ranar Talata, 3 ga watan Yuni, 2014.
Amarya ta kwakule idon kishiyarta
Wata amarya da aka yi bikinta watanni uku da suka wuce a unguwar Hammadu Kafi a garin Gombe, mai suna Zainab Haruna, mai kimanin shekaru…