Daga John C. Azu
Alƙalin babbar kotun tarayya dake Abuja, Mai Sharia James Omotosho ya ƙi sa hannu a takardar sakin jami’in ɗan sanda DCP Abba Kyari duk da bayar da belinsa da ya yi kan N50 miliyan.
Mai Sharia Omotosho ya bayar da belin DCP Abba Kyari wanda ya shafe watanni 18 a kurkukun Kuje, Abuja bisa tuhumar rashin bayyana kadarar da ya mallaka.
Sai dai alƙalin ya ce ba zai sa hannu a sake shi ba har sai an bada belinsa a wasu shari’o’in da ya ke fuskanta da su ka danganci safarar muggan ƙwayoyi.
Kotu ta bayar da belin Abba Kyari bayan wata 18 a gidan yari
‘Abba Kyari ya yi min tayin N10m don na yi wa Saraki kazafi’
A ranar 23 ga Maris ne dai Mai Sharia Emeka Nwite ya ƙi bada belin DCP Kyari a karo na biyu game da zargin safarar ƙwayoyi da ake yi masa tare da wasu jami’an ƴan sanda.
DCP Kyari wanda ya yi suna wurin yaƙi da masu garkuwa da mutane ya musanta tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Sai dai farar hula biyu da aka tuhume su tare Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsusu Ezenwanne sun amsa laifin har ma an zartar musu da hukuncin ɗaurin shekaru biyu-biyu a kurkuku.
Mai shari’a Omotosho ya ɗage sauraron ƙarar da ke gabansa har zuwa 18 ga Oktoba.