Daya daga cikin manyan wadanda ake zargi da yin fashi da makami a wani banki da ke garin Offa a Jihar Kwara, Ayoade Akinnibosun, ya bayyana yadda dakataccen jami’in dan sandan nan DCP Abba Kyari ya yi masa tayin naira miliyan 10 da kuma biza ta fita ketare don ya yi wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki kazafi.
Wanda ake zargin an gurfanar da shi a gaban kotu tare da wasu mutum biyu kan zargin hada baki, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma kashe jami’an ’yan sanda tara a yayin fashin bankin.
- Mutum 2 sun rasu yayin turereniya a filin kwallon kafar Iraqi
- Kuskuren shekara 24 ne ya jefa Najeriya halin da ta ke ciki — Kwankwaso
Ya bayyana wa wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Ilorin yadda Abba Kyari ya yi masa romon baka don ya danganta Saraki da fashin bankin da suka yi.
Akinninbosun ya ce, “Ya bukaci na yi tunani sosai kan tayin da ya yi min. A nan ne ya umarci wasu jami’ai biyu; Hassan da Mashood su mayar da ni wani kurkuku na daban. Sannan ya bayar da umarnin a daina azabtar da ni,” in ji shi.
Wanda ake zargin, ya ce ba a bar shi ya rubuta jawabinsa ba baya ga sunansa da aka dauka a Ilorin har sai da aka kai shi Abuja a cikin wata bakar mota.
Kazalika, ya ce a kan idonsa Abba Kyari ya sa aka harbe wasu Fulani makiyaya sannan ya sa aka harbe shi a kafa kan dole sai ya alakanta Saraki da fashin da suka yi a garin Offa.
Wanda ake zargin ya nuna wa kotu raunin harbin bindigar da aka yi masa a ranar Laraba.
Akinninbosun, ya bayyana yadda a kan idonsa aka harbe wansa, Micheal Adikwu wanda yana daya daga cikin wadanda suka aikata fashin bankin Offa tare, lamarin da ya razana shi har sai da ya amince da tayin da Abba Kyari ya yi masa.
Sai dai Mai shari’a Alimat Salman, ta dage sauraren karar har zuwa ranar 13 ga watan Fabrairu, 2023.
Aminiya ya ruwaito cewa, tun a watan Fabrairun bara ne dai wasu gungun ’yan fashi da makami suka kai hari wani banki da ke Unguwar Uromi a yankin Offa na Karamar Hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a Jihar Edo.