Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta ki amincewa da bukatar neman beli wadda dakataccen Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, DCP Abba Kyari ya gabatar.
Aminiya ta ruwaito cewa, alkalin kotun Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin.
A maimakon haka, alkalin ya umarci da a hanzarta shari’ar a yayin da mai gabatar da kara ya ankarar da shi cewa Kyari da sauran wadanda ake tuhuma na iya yi wa shari’ar bita-da-kulli.
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta NDLEA ce dai ta gurfanar da Abba Kyari tare da wasu mutum shida kan zargin badakalar hodar iblis.
Ana iya tuna cewa, gabanin shigarsa hannu, Hukumar NDLEA din ce ta ayyana neman Kyari bayan da ta samu faifan bidiyo da ke nuna yadda ya ke tattaunawa da masu bincikenta kan cinikin kwayoyi.
An kama sauran wadanda ake tuhumar ne a ranar 19 ga watan Janairu a filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke Jihar Enugu, inda suka amsa cewa su ne masu jigilar kwayoyi.
A cikin tuhume-tuhumen, Abba Kyari, ACP Sunday Ubua, ASP Bawa James, Insifeto Simon Agirigba, da Insifekta John Nuhu, an ce dukkansu jami’an hukumar leken asiri ta Intelligence Response Team (IRT) sun yi cinikin hodar iblis mai nauyin kilogiram 17.55 tsakanin ranar 19 zuwa 25 ga watan Janairu.
Tun a watan Fabrairu ne ne Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kama Abba Kyari ta kuma mika wa Hukumar NDLEA wadda ta yi shelar neman sa ruwa a jallo, bayan ya ki amsa gayyata domin ba da ba’asi dangane da zargin da ake masa na alaka da masu safarar kwayoyi.