A wani mataki na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, al’ummomin Goska da Dangoma da ke Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.
An rattaba hannun ne a garin Dangoma tare da bikin mika cibiyar sauraron koke-koke game da laifuffukan cin zarafin mata da kananan yara da saurarnsu wacce kungiyar Global Peace Development (GDP) ta gina tare da tallafi daga kungiyar International Alert.
Daraktan Gudanarwa na kungiyar GPD ta kasa, Ebruke Onajite Esike, ya jaddada muhimmancin wannan shirin, inda ya ce suna gudanar da irin aikin ne a al’ummomi biyar da ke kananan hukumomin Chikun da Jama’a wadanda suka fuskanci matsalolin rikice-rikice da tashin hankali a baya.
A shekarar da ta gabata, GPD tare da tallafin daga International Alert, sun taimaka wa mutane 3,396 ta hanyar shirye-shirye daban-daban da suka hada da wayar da kan jama’a da ba su horo da tattaunawa da samar da Tsarin Zaman Lafiya da Sulhu na Mata.
Shirye-shiryen sun taimaka wajen magance muhimman abubuwan da suka shafi cin zarafin jinsi da haifar da zaman lafiya mai dorewa.
Wani bangare mai muhimmanci da aka rattaba hannu a kai shi ne kirkirar Kwamitin Zaman Lafiya na Hadin Gwiwa, wanda zai rika kula da ayyukan makiyaya, tabbatar da bin dokokin al’umma, da kuma karfafa zaman tare don inganta fahimtar juna da kuma hana aukuwar rikice-rikice a nan gaba a yankunan biyu.
Da yake jawabi a madadin Daraktan kungiyar International Alert, Sunday Momoh Jimoh, Manajan Ayyuka a International Alert, ya nuna matukar godiyarsa da irin hadin kan da al’ummomin jihar Kaduna suka ba su tare da yaba musu yadda har suka zama abin koyi ga wasu jihohin.
Tun da farko a cikin jawabinsa, shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Yunana Markus Barde, ya gode wa Allah bisa zaman lafiyar da aka samu a yankin.
Sannan ya roki mazauna yankin da su ci gaba da bayar da cikakken goyon baya da hadin kai ga hukumomin gwamnati wajen wanzar da zaman lafiya, tare da yin kira ga Musulmai da Kiristoci da su rungumi zaman lafiya a kodayaushe.
A sakonsa na fatan alheri, Hakimin masarautar Nikyob (Kaninkon), wanda Dagacin Unguwan Tudu, Benedict Bala Bin, ya wakilta, ya yaba wa kungiyoyin inda ya roke da su fadada ayyukansu ga sauran al’ummomin masarautar.
Dagacin Dangoma da na Goska ne suka jagoranci al’ummomin su wajen rattaba hannu a madadin dukkan bangarorin biyu.