Gamayyar al’ummar Tudun Murtala da ke Kano sun dukufa wajen gyara makabartarsu, wadda duk lokacin damina ruwa yakan wanke kaburbura ya bude su, sannan ya fito da da yawa daga cikin gawarwakin da ke kwance a ciki, inda a wasu lokutan ma ruwan ke tafiya da wasu gawarwakin har su bace.
A cewar daya daga cikin matasan unguwar, Malam Bello Sagir, ya ce tun da aka kafa wannan unguwar babu wata matsala da ta addabi mutanen yankin kamar wannan matsalar, domin duk dan unguwar, a kullum da matsalar yake kwana yake tashi.
A watan Satumbar bana, Aminiya ta ruwaito yadda zaizayar kasa ke neman lalata makabartar ta Tudun Murtala, a wani rahoto na musamman bayan Aminiya ta ziyarci makabartar.
A wancan rahoton, Alhaji Lawan, wanda shi ne ma’ajin kwamitin kula da makabartar ya nuna yadda suka sanar da gwamnati tun daga matakin karamar hukuma zuwa jiha amma babu abin da aka yi. Shi ya sa wannan karon suka mike suka tara kwabo da sisi, suka fara gabatar da aikin gyaran makabartar ka’in da na’in.
Hakazalika, sun nuna rashin amfanin ofishin mataimakin gwamnan jihar a kan harkar makabartu. “Tun daga kafa wannan ofishin zuwa yanzu, babu wani abin kirki da ya yi. Don haka ne muke kira ga mai girma gwamna da ya gaggauta rushe wannan ofishin ko kuma shi mai rike da ofishin ya sauka domin ya tsira da mutuncinsa,” inji Sagir Bello.
Ya kara da cewa: “’Yan unguwar suna iyakacin kokarinsu wajen wannan aiki. Aikin gyaran makabartar yana bukatar makudan kudi. Shi ya sa muke neman tallafin kuma ga masu son ba da taimakon, za su iya neman kwamitin kula da makabartar domin su bayar da nasu.”
Daga karshe sai ya ce yana mika godiya ta musamman ga dukan mutanen unguwar, da ma wadanda ba ’yan unguwar ba da suke taimakawa ta hanyoyi daban-daban don ganin an kawo karshen wannan matsalar.