Gamayyar kungiyoyin al’umma da ke garin Dolen Machina a Karamar Hukumar Machina ta Jihar Yobe, sun roki Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmed Lawan ya kawo musu dauki kan matsalar ruwan shan da ta addabe su.
Mutanen, wadanda suna cikin mazabar Yobe ta Arewa wacce Sanatan ke Wakilta a Majalisar sun ce suna cikin halin tsaka mai wuya saboda matsalar ruwan shan.
- Mun kashe ’Yan Najeriya 38 da ke taimakon Ukraine a yaki —Rasha
- ’Yan bindiga sun kai wa maniyyata Aikin Hajji hari a Sakkwato
Rokon nasu dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da suka fitar dauke da sa hannun Shugaban gamayyar kungiyoyin garin, Malam Umar Alhaji Malu Dolen Machina a Kano ranar Litinin bayan wani taro.
Sanarwar ta ce duk da yake al’ummomin na sane da cewa Sanatan ba a bangaren zartarwa yake ba, amma yana da alfarmar da zai mika kokensu ga inda ya dace don a share musu hawaye.
Sun ce garin nasu ya jima yana fuskantar koma-baya a kusan dukkan abubuwan more rayuwa.
Sun ce, “Mun bi ta hanyan duk wani mai ruwa da tsaki a yankin don a share mana hawaye amma kakar mu ta gaza cim ma ruwa.
“Yankinmu yana cikin kunci, ba mu san wani romon Dimokuradiyya ba cikin shekara 23 da Najeriya ta yi, shi ya sa muke kira ga Sanatanmu, kuma Shugaban Majalisar Dattawa ya kawo mana agaji,” inji sanarwar.