✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’ummar kauyen Kundulum za su gina gada ta biyu

Al’ummar kauyen Kundulum da ke karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe sun yunkuro wajen sake gina wata gada ta biyu ta shiga garin ta aikin…

Al’ummar kauyen Kundulum da ke karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe sun yunkuro wajen sake gina wata gada ta biyu ta shiga garin ta aikin gayya bayan sun kammala ta farko.

Da yake zantawa da Aminiya a wajen aikin gina gadar, Hakimin Kundulum Alhaji Shu’aibu Muhammed, ya bayyana cewa bai san wane irin bayani zai yi ba saboda murna da farin ciki na yadda al’ummar sa suka hada kai suke ciyar da wannan gari nasu gaba.

Duk da yake aiki ne na gayya amma sun hada gwiwa da hukumar nan mai bada tallalfi wajen aikin gayya ta CSDP Community and social debelopment project.

Ya ce suna rokon gwamnan Jihar Gombe, idan suka kammala wannan aikin gada da ya samar musu da karamar Makarantar Sakandare a garin don bunkasa harkar ilimi a tsakanin ‘ya’yansu.

Hakimin ya kara da cewa wannan gari manoma, suna son a samar musu da hanya wacce za ta sawwake wa al’ummar yankin wajen sufuri domin a lokacin kaka suna fitar da amfanin gona na miliyoyin naira amma ba su da hanya, wanda ya sa manoman suke shan wahala.

Adamu Lamido, shi ne wakilin karamar Hukumar Akko, kuma jami’i ne a bangaren kula da walwala na karamar Hukumar wato desk officer na CDSP cewa ya yi kafin a fara wannan aikin gayya, karamar Hukumar Akko tana taimakawa yankin don ganin sun sami yadda za su yi. Sannan ya godewa mutanen garin bisa wannan kokari da suka yi.

Shi ma Ibrahim Shu’aibu walin Kundulum, wanda shi ne shugaban gudanarwa na wannan aiki, ya ce kafin hukumar CSDP ta kawo musu tallafi tuni suka fara tara kudade a tsakaninsu sannan suka tunkari hukumar.

Ya ce an kiyasta wannan aikin zai ci naira miliyan goma amma su sun bada kashi goma ne na aiki CSDP ta basu kashi 90 wanda kuma kudin zai ishesu su gama aikin.

Haruna Muhammad Isa, shugaban tattara kudade, ya ce sai da suka tara naira miliyan daya daga kungiyoyi goma da suke da su a yankin na Kundulum da Kurba har zuwa Kwami kafin su kai kan sauran jama’a.

Daga nan sai ya yi amfani da wanann damar wajen jan hankalin mutane da cewa wannan aikin nasu na gayya ne amma sun ji wani ya shiga Radiyo Progress FM yana cewa wai wani dan siyasa ne mai neman gwamna a jihar ya yi musu.