A karo na farko tun bayan tserewar Yahya Jammeh gudun hijira shekara kusan biyar da suka wuce, al’ummar Gambiya na zaben shugaban kasa.
Ga Shugaba Adama Barrow, wanda ke neman ta-zarce, wannan zabe gwaji ne na gamsuwar al’umma da kokarinsa na kawo cigaban kasa.
Bayan shi kuma, mutum biyar ne ke takara ko da yake an fi ganin tsohon dan siyasa mai shekara 73, Ousainou Darboe, a matsayin babban dan takarar bangaren adawa.
Darboe, wanda lauya ne da ya kare mutanen da suka yi adawa da Jammeh, ya sha kalubalantar tsohon shugaban kasar a zabe.
Ya kuma rike mukamin Ministan Harkokin Waje sannan Mataimakin Shugaban Kasa a karkashin Adama Barrow kafin ya yi murabus a 2019.
Darboe ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Barrow ya gaza, kuma a maimakon ya gina dimokuradiyya, ya fi mayar da hankali ne wajen kare mulkinsa.
Tasirin Jammeh
Al’ummar kasar ta Gambiya dai na fatan samun sauyin rayuwa, amma har yanzu ana jin tasirin Jammeh, wanda ya kwace mulki a 1994 ya kuma yi shekara 22 yana kama-karya, a fagen siyasar kasar.
Yiwuwar dawowarsa daga gudun hijira da abin da ya kamata a yi game da zarge-zargen aikata munanan laifuffuka a zamaninsa – ciki har da fyade, da azabtar da mutane, da amfani da ’yan ina-da-kisa – na cikin batutuwan da suka fi jan hankali gabanin zaben.
A watan Janairun 2017 aka tilasta wa Jammeh tafiya gudun hijira a Equatorial Guinea bayan da Shugaba Adama Barrow, wanda a lokacin ba a san shi sosai ba, ya kayar da shi a zabe.
Sai dai har yanzu yana da magoya baya wadanda suke fadi-tashin ganin ya koma gida.
Ya kuma yi yunkurin jan akalar zaben ta hanyar yin magana da dimbin magoya bayansa ta wayar tarho yayin tarurrukan gangamin da aka gudanar.
Zakaran gwajin dafi
Wasu manazarta dai na kallon zaben a matsayin zakaran gwajin dafi ga dimokuradiyyar kasar wadda ke tatata.
Gambiya na cikin kasashen da suka fi talauci a duniya – a cewar Bankin Duniya, kusan rabin al’ummar kasar, wadanda yawansu ya kai miliyan biyu, suna rayuwa ne a kan kasa da Dala 1.90 a kullum.
’Yan Gambiya da dama da suka zanta da AFP sun ce tattalin arziki ne batun da ya fi ci musu tuwo a kwarya.
“Ina jin jiki”, inji Abdoulaye Janneh, wani elektirisha mai shekara 27 a kusa da Banjul, babban birnin kasar.
Ya kara da cewa gwamnati mai ci ta yi alkawarin samar da ayyukan yi, musamman ga matasa, amma har yanzu shiru ake ji.
Alkawari kaya ne
A karkashin mulkin Barrow dai an soke hukuncin kisa, an saki fursunonin siyasa, sannan an assasa tsarin dimokuradiyya mai jam’iyyu da dama.
Bugu da kari, Gambiya ta shigar da kara a gaban Kotun Duniya tana zargin Myanmar da kisan kare dangi a kan Musulman Rohingya.
Sai dai shugaban kasar mai ci yana shan suka bisa zargin da wasu ke yi cewa yana shirya tuggu don gyara siyasarsa nan gaba.
Barrow dai ya lashe zabe ne a 2016 lokacin da wata gamayyar ’yan adawa ta goya mishi baya bisa alkawarin cewa zai sauka bayan shekara uku.
Amma ya saba alkawari ya yi shekara biyar din da Kundin Tsarin Mulki ya tanada, lamarin da ya jawo munanan zanga-zanga a wasu lokuta.
Ce-ce-ku-ce
Bugu da kari jam’iyyar NPP ta Barrow ta kulla kawance da APRC ta Yahya Jammeh – matakin da wasu ke kallon makarkashiya ce don cin zabe, kuma masu fafutuka suka yi tir da shi.
Sai dai Jammeh ya ce bai san wannan magana ba, kuma tuni magoya bayansa suka kirkiri wata sabuwar jam’iyyar adawa.
Matakin dai ya haddasa shakku game da aniyar Barrow ta hukunta wadanda suka aikata manyan laifuffuka a zamanin Jammeh.
Sakamako
Da karfe 9 na safe agogon Najeriya ake sa ran bude rumfunan zabe, a kuma rufe kada kuri’a da karfe 6 na yamma agogon Najeriya.
Zaben dai kifa daya kwala ne kuma akwai yiwuwar samun sakamakon farko ranar Lahadi.