✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Al’ummar Filato sun koka kan karuwar matsalar tsaro

Al’ummar unguwar Mista Ali da ke Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato sun koka kan yawaitar ayyukan ’yan fashi da masu garkuwa da mutane a…

Al’ummar unguwar Mista Ali da ke Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato sun koka kan yawaitar ayyukan ’yan fashi da masu garkuwa da mutane a yankin.

Karuwar matsalar ta sa Kansilan yankin, Murtala Abdullahi, ya kira taron masu ruwa-da-tsaki a fadar basaraken yankin, Cif Danladi Maikinga Kasuwa, da nufin lalubo mafita.

Ya shaida wa taron, wanda Babban Jami’in Dan Sanda Mai Kula da Shiyyar Bassa ya halarta cewa, “A fili yake cewa yanzu babu wadatattun jami’an tsaro a yankinmu.

“Don haka ya zama wajibi ’yan banga da al’ummar wannan yanki su tashi su kare rayuka da dukiyoyinsu.”

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da ke yankin da su tashi haikan wajen gudanar da aikinsu na kare al’umma, tare da rokon jama’a su mara musu baya.

Kansilan ya kuma roki kwamishinan ’yan sandan Jihar Filato da ya kafa Babban Ofishin ’Yan Sanda a garin Jingir.

A jawabinsa, basaraken yankin Mista Ali, ya bai wa jami’an tsaro tabbacin samun goyon baya da hadin kan al’ummarsa wajen tabbatar da tsaro da kuma yakar ’yan fashi da masu garkuwa da mutane.

A nasa bangaren, DPO na yankin, Samuel, ya ba da tabbacin shirin ’yan sanda na yin aiki tare da mutanen yankin domin magance matsalolin tsaro da ke ci musu tuwo a kwarya.