Al’ummar garin Farakwai da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna sun koka tare da zargin Kamfanin ZEBERCED da gurbata muhallinsu da kuma rayuwarsu, sanadiyar aikin fasa duwatsu da yake yi a yankin.
Al’ummar sun yi wannan koke ne a lokacin da suke zantawa da wakilin Aminiya a kan zargin da suke yi na hada baki da dagacin yankin don kuntata wa rayuwarsu da lafiyarsu da muhallinsu.
Sun kuma zargi Dakacin Farakwai, Alhaji Muhammad Labaran da yin sama-da-fadi da tallafin da Kamfanin ZEBERCED ke bayarwa duk shekara domin kyautata dangantakarsa da al’ummar yankin.
Mai magana da yawun al’ummar, Aminu Tukur Kwanar Farakwai ya shaida wa Aminiya cewa shekara biyar ke nan da Kamfanin ZEBERCED ya fara aiki a yankin kuma bai taba saba wa bayar da tallafin ba.
- Kwaso ’yan Najeriya: Jami’an ofishin jakadancin Najeriya sun tsere daga Sudan —Dalibai
- Yau ’yan Najeriya 1,500 da suka makale a Sudan za su iso Abuja
Ya ce a shekara hudu da suka gabata, kudin kamfanin yake bayarwa sai a bana saboda halin matsi da tattalin arziki ya shiga, ya bayar da shinkafa don a raba wa al’ummar.
Aminu ya ce, “Ko a lokutan da aka ba da kudin, Dagacin akwai nasa kason na daban, shi da sauran dagatai ’yan uwansa da kuma na iyalansa har mutum 11 da ake ba su.
“Amma duk da haka idan ya karbi nasa kudin, Naira dubu 100 da na iyalansa 11 Naira dubu 50, sai na talakawa su 100, Naira dubu 50 amma wadanda yake sa su bi layi a ba su kudin, sai ya bi su ya karbe; ya ba su Naira dubu biyar-biyar sauran ya rike.
“Haka abin ke faruwa kuma duk lokacin da ake kokarin fahimtar da shi, sai dai ya yi ta zage-zage da barazanar cewa sai ya ga bayan mutum.”
Ya ce, “A wannan karo mun kafa kwamiti daga cikin al’ummar Farakwai domin gudanar da rabon shinkafar amma sai shi Sarkin Farakwai ya ce ba ruwansu da kwamitin da masu unguwaninsa zai yi aiki, kuma hakan ya yi.”
Al’ummar sun zargi Dakacin da cewa an ba shi buhun shinkafa 40 amma ya bai wa masu unguwaninsa hudu buhuna 3 kowanensu, tare da umurtar su da su dauki rabin buhu, su raba wa talakawansu buhu biyu da rabi.
A cewar al’ummar, kasancewar gonakinsu na fuskantar barazanar garin dutse idan suka zo noma kuma karfin nakiyar fasa dutsen na barazana ga gidajensu amma Sarkin Farakwai Alhaji Muhammad Labaran bai yi wani motsi ta yadda zai jagoranci wakilan al’ummar zuwa Kamfanin ZEBERCED don tattaunawa da su ba, kuma idan ya je kamfanin ko an kira shi bai sanar da al’ummarsa abin da suka tattauna sai ya bar wa cikinsa.
Haka kuma sun koka cewa wasu daga cikin al’ummar da suke kusa da kamfanin yanzu haka suna fuskantar matsalolin ciwon ido da ciwon Asma saboda burbushin garin dutsen da ake fasawa.
Da yake bayani kan korafin al’ummar, Sarkin Farakwai Alhaji Muhammad Labaran ya ce shi buhun shinkafa 30 ya karba kuma akwai masu unguwanni 11 a karkashisa. Ya ba kowannensu buhu 3 na shinkafa, ya ce su dauki rabin buhu su raba buhu biyu da rabi ga al’ummarsu.
Ya musanta cewa ya ki yi musu jagora zuwa kamfanin. Ya ce hasali ma babu wanda ya taba samunsa ko a rabuce domin ya jagorance su zuwa wajen mahukunta kamfanin na ZEBERCED, kan wata matsala da suke kokawa a kai.
Da Aminiya ta tuntubi daya daga cikin mahukuntan kamfanin, Alhaji Aliyu ta wayar hannu, ya ce wannan matsala ce ta tsakanin al’ummar Farakwai da Dakacinsu, su je su kai koke wajen hakiminsu.